APC: Abubuwa 3 da Suka Hana a Ga Bola Tinubu a Taron ‘Yan Takaran Shugaban Kasa
- Bola Ahmed Tinubu ya yi bayanin abin da ya sa bai halarci zaman da aka yi da masu neman takara ba
- Sanarwar ta fito ne ta ofishin Festus Keyamo wanda shi ne Kakakin Kwamitin yakin neman zaben APC
- Keyamo yace Tinubu bai da sararin halartar zaman, sannan bai son nuna son-kai ga sauran gidajen labarai
Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar APC ya fitar da jawabi a kan rashin halartar taron da aka yi da masu neman mulki.
A wata sanarwa da ta fito daga bakin Festus Keyamo, an ji cewa Bola Ahmed Tinubu yana da wasu abubuwan da suka hana shi zuwa taron jiya da aka yi.
Darektan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Festus Keyamo yace ‘dan takaransu yana ta faman ganawa da jama’a kai-tsaye.
2023: Tinubu Ya Fi Duk Sauran Yan Takarar Shugaban Kasa Cikakken Lafiya – Kungiyar Yakin Neman Zaben APC
A matsayinsa na kakakin kamfe, Ministan ya jero uzurin ‘dan takaran. Bashir Ahmad wanda hadimin shugaban kasa ne ya wallafa sanarwar a shafinsa.
Dalilan da Festus Keyamo ya bada
Na farko, gidajen rediyo da talabijin da-dama a Najeriya sun nuna sha’awar kiran irin muhawarar nan, ‘dan takaranmu ba zai fifita wasu gidajen, ya yi watsi da wasu ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan ya samu damar zama shugaban Najeriya, ya yi niyyar yi wa kowa adalci da gaskiya.
Na biyu kuma, karancin lokaci da yanayin yakin takarar Asiwaju Tinubu ba zai ba shi damar halartar duka wadannan taro da gidajen rediyo da talabijin ba.
Wannan ya sa mu ka dauki mataki ba za a fara da wani gidan talabijin, ayi watsi da wasu ba.
Na uku, tuni ‘dan takaran ya san muhimmancin tattaunawa da ‘Yan Najeriya kai-tsaye, jim kadan bayan gabatar da manufofinsa, ya fara zama da jama’a.
(Tinubu) ya zauna da ‘yan kasuwa a Kano, sannan da kwararru a Legas a makon jiya. Gobe (Litinin) zai hadu da kungiyoyin ‘yan kasuwa a Minna, jihar Neja."
- Festus Keyamo
Daily Trust ta rahoto kwamitin ya godewa gidan talabijin Arise da suka shirya wannan taro, yace za a ji daga bakin ‘dan takaran na APC a wasu wuraren dabam.
Wannan ya nuna tsohon Gwamnan ba zai taba amsa goron gayyatar irin wannan taro ba.
Okowa ya Wakilci Atiku
A ranar Lahadi ne aka samu labari an yi taro na musamman domin jin manufofin 'Yan takaran Shugaban kasa a zaben 2023 kan batun tsaro da tattalin arziki.
Har aka tashi ba a ga Asiwaju Bola Tinubu da Atiku Abubakar a wajen zaman ba. Amma Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun yi baja-kolin manufofinsu.
Asali: Legit.ng