2023: Tinubu Ya Fi Duk Sauran Yan Takarar Shugaban Kasa Cikakken Lafiya – Kungiyar Yakin Neman Zaben APC
- Kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC ta ce Asiwaju Bola Tinubu na da koshin lafiya baida wata matsala da lafiyarsa
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ce Tinubu ya fi duk sauran masu neman kujerar Buhari lafiyar jiki da na kwakwalwa
- Fani-Kayode ya ce babbar jam'iyyar adawar kasar ta tsorata da shahara da karfin dan takarar na APC shiyasa suka koma kan lafiya da shekarunsa
Abuja - Kungiyar yankin neman zaben Shettima/Tinubu ta ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na da isasshen lafiya, rahoton Nigerian Tribune.
A wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ce Tinubu ya fi sauran yan takarar shugaban kasa lafiyar jiki da na kwakwalwa.
Fani-Kayode shine daraktan kula da shafukan zumuntan zamani na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC.
Ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Tinubu na da isasshen lafiya kuma bai da wani abun boyewa saboda babu guntun kashi a tsuliyarsa·
"Baya ziyartan yan bori, shi tsarkakke ne ciki da bai, duk abun da za a fadi game da Tinubu, bai taba yaudarar mutanen da suka taimake shi har ya hau karagar mulki ba, yana biyayya ga mutanensa sosai.
"A kulla yaumin, rashin sani, son zuciya da raunin masu adawa yana kara fitowa fili."
Fani-Kayode ya ce jam'iyyar PDP na tsoron shahara da damammakin da Tinubu yake da su a zaben, rahoton TheCable.
Ya ce sakamakon haka, PDP ta koma gaba da lafiya da shekarunsa.
"Jam'iyyar PDP da dan takatarta na shugaban kasa, Atiku Abubakar sun san cewa Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2023, hakan na kara bayyana a kulla yaumin.
"Wannan ne yasa suka firgita, shine dalilin fa yasa suka koma yin karya, zage-zage da cin mutunci.
"Shiyasa abu daya da suke magana akai shine lafiya da shekarun Tinubu."
Ya ce kwamitin kamfen din APC ba zata bari maganganu marasa dadi da sukar abokan hamayya ya janye mata hankali ba, yana mai cewa za su mayar da hankali inda suka sa a gaba.
Shugaban Masu Rinjaye A Majalisar Wakilai Doguwa Ya Magantu Game Da Batun Sauya Shekarsa Daga APC
A wani labarin, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne kuma bai da wani dalili na barin jam’iyyar imma a yanzu ko a nan gaba.
Ya ce wadanda ke zargin yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar suna yada labaran karya ne kawai.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Tunde Rahman, hadimin dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya aikewa Legit.ng a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba.
2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi
Asali: Legit.ng