Ado Doguwa Ya Sake Tone-Tone a Kano, Yace Dan Takarar Mataimakin Gwamna Na Yi Wa Atiku Aiki
- Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin tarayya, Alhassan Doguwa, ya sake jefa zargi kan Murtala Sule Garo
- Ɗan majalisar ya yi ikirarin cewa ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano na APC na cin amanar jam'iyyar ta karkashin kasa
- Wannan na zuwa ne yayin da ake tsaka da dambarwa a APC reshen Kano musamman tsakanin Doguwa da Garo
Kano - Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin tarayya, Alhassan Doguwa (APC, Kano) ya zargi ɗan takarar mataimakin gwamna a Kano karkashin APC, Murtala Sule Garo, da yi wa Atiku aiki ta karkashin ƙasa.
Yayin hira da manema labarai ranar Jumu'a, Doguwa ya yi ikirarin cewa Garo na yi wa surukinsa aiki bayan gaza samun tikitin gwamna saboda yana auren Walida Atiku.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an ɗaura auren Garo da ɗiyar ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, tun shekarar 2016 a Yola.
Ɗan majalisar ya bayyana cewa Mista Garo, tsohon kwamishinan kananan hukumomi, ya taɓa bashi amanar cewa ya fi kaunar zama surukin shugaban ƙasa fiye da mataimakin gwamna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Doguwa yace:
"Amaryarsa ɗiyar Atiku ce, lokacin da aka hana shi takarar gwamna. Na kai masa ziyara, a lokacin ya faɗa mun tunda abun haka ne ya gwammace ya zama surukin shugaban kasa da mataimakin gwamna da za'a maida shi ɗan aike."
"Wannan itace matsayar yaron, cin amanar da yake yi yau, na rantse da mahalicci na zuciyarsa bata tare da APC, burinsa ya zama surukin shugaban ƙasa kuma ina da yaƙinin haka ba zata faru ba."
"Shugaban ƙasar Najeriya a yanzu shi ne, Muhammadu Buhari, kuma shugaban da zai gaji Buhari da ikon Allah shi ne, Sanata Bola Ahmed Tinubu."
Sai dai Doguwa bai nuna wata kwakkwarar shaida da zata tabbatar da wannan zargin nasa ga yan jarida ba, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Me Sule Garo ya faɗa game da wannan zargin?
Har zuwa yanzun Sule Garo bai maida martani kan wannan sabon zargin ba. Yayin da jaridar ta nemi jin ta bakinsa, bai amsa kiran waya ko turo amsar sakonnin da aka tura masa ba.
Legit.ng Hausa ta gano cewa wannam zargin na zuwa ne yayin da wutar rikici ke ci gaba da ruruwa a jam'iyyar APC reshen jihar Kano.
A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Nemi Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Janye, Ya Mara Wa PDP Baya a 2023
Tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ta nemi ɗan takarar LP, Peter Obi ya aje takara ya marawa PDP baya a 2023.
Kakakin PCC, Sanata Dino Melaye, yace Obi ba zai iya cin nasara a zaben da ke tafe ba saboda a iya yanki ɗaya ya yi suna.
Asali: Legit.ng