Rikicin Afenifere: Kungiyar Yarbawa Ta Ragargaji Tinubu, Ta Masa Lakabi Da 'Babban Mai Raba Kawuna'

Rikicin Afenifere: Kungiyar Yarbawa Ta Ragargaji Tinubu, Ta Masa Lakabi Da 'Babban Mai Raba Kawuna'

  • Kungiyar Southwest Renaissance Group ta zargi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Ahmed Bola da raba kan yan Afenifere
  • Kungiyar ta gargadi mutanen kudu maso yamma kada su goyi bayan tsohon gwamnan na jihar Legas
  • A cewar kungiyar, Tinubu ya saba raba kan shugabannin yarbawa domin cimma burinsa na siyasa

FCT, Abuja - Kungiyar al'ummar yarbawa ta Southwest Renaissance Group ta soki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Peoples Congress, APC, kan rikicin da ke faruwa a Afenifere.

A wani sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar, Honarabul Olaitan Abdul Salam kuma ya tura wa Legit.ng a ranar Asabar, 5 ga watan Nuwamba, kungiyar ta bayyana dan takarar na APC a matsayin 'babban mai raba kawuna'.

Bola Tinubu
Rikicin Afenifere: Kungiyar Yarbawa Ta Ragargaji Tinubu, Ta Masa Lakabi Da 'Babban Mai Raba Kawuna'. Hoto: @OfficialBAT.
Asali: Facebook

Kungiyar ta ci gaba da cewa Tinubu mutum ne mai kaurin suna wajen kawo rarraba kawunan mutane da kawo rashin zaman lafiya, tana mai gargadin Yarabawa su yi taka-tsan-tsan wajen baiwa tsohon gwamnan jihar Legas goyon bayansu a zaben da ta ke tafe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Hakan na zuwa ne bayan wani shugaban Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya bayyana a fili cewa kungiyar na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi, rahoton Legit.ng.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce:

"Ba mu yi mamakin abin da ke faruwa a yanzu ba, mun san shi sosai a matsayin wanda ya saba raba kan mutane.
"A 2002, shi dai Bola Tinubun ya raba kan Afenifere domin samun nasararsa a matsayin gwamnan Legas karo na biyu.
"Ya raba kan kwamitin dattawan Yarbawa a 2015 don ya rika juya yarbawa; kuma ya raba kan Afenifere saboda takararsa na shugaban kasa a 2023.
"Dole ne mu kubutar da kasarmu daga wannan babban mai raba kan mutane kuma mu tabbatar da cewa shigar da Yarbawa cikin siyasar Najeriya ba za ta kasance bisa kabilanci ba amma bisa zaben shugaban da ya cancanci a matsayin 'Omoluabi'".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164