Kotu Ta Tunbuke Wani Dan Takarar Shugaban Kasa a Babban Zaben 2023
- Babbar Kotun tarayya dake zama a Abuja ta soke tikitin baki ɗaya yan takarar da jam'iyyar AA karkashin Kenneth Udeze ta miƙa wa INEC
- Alkalin Kotun yace INEC ta tafka kuskure bisa karban sunayen ciki harda ɗan takarar shugaban kasa, Hamza Al-Mustapha
- Hukuncin ya umarci INEC ta karɓa tare da ayyana sunayen yan takara da tsagin AA karkashin Omoaje ya miƙa
Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zama a Abuja ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta cire sunayen yan takarar jam'iyyar Action Alliance (AA).
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Kotun ta nemi INEC ta goge sunayen waɗanda tsagin AA na Kenneth Udeze ya miƙa mata, ciki harda ɗan takarar shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya.
A takardar Hokuncin Kotun da ta shiga hannun yan jarida yau Asabar a Kaduna, Kotun ta umarci INEC ta gaggauta karɓa tare da bayyana sunayen 'yan takarar da tsagin jam'iyyar AA karkashin Adekunle Rufai Omoaje ya miƙa mata.
Alkalin Kotun mai shari'a Z.B Abubakar, yace hukumar zaɓe ta tafka Kuskure bisa rashin amincewa da jerin sunayen 'yan takara wanda tsagin Mista Omoaje, ya miƙa mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Omoaje a madadin jam'iyyar AA ya garzaya Kotun inda ya roki ta gyara kuskuren da INEC ta yi na ƙin amincewa da sunayen yan takarar da ya miƙa mata.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sakamakon wannan hukuncin jerin sunayen yan takarar AA da tsagin Omoaje ya miƙa zasu maye gurbin waɗanda hukumar zaɓe INEC ta riga ta sanar.
Daga cikin 'yan takarar da zasu rasa damar shiga zaɓen 2023 bayan wannan hukunci harda Manjo Al-Mustpah mai ritaya wanda jam'iyyar AA ta ayyana a matsayin ɗan takararta na shugaban kasa.
Haka zalika duk da INEC ta fitar da sunansa a shafinta na yanar gizo, mai yuwuwa hukuncin Ƙotun ya sa a sauya sunan Al-Mustapha da wani daban wanda tsagin Omoaje ya amince da shi.
Da yake tsokaci game da hukuncin, shugaban AA na ƙasa, Adekunle Omoaje, yace Kenneth Udeze mai cewa shi ne shugaban jam'iyya am kore shi tun watam Fabrairu, 2020.
Tsohuwar shugabar matan PDP a Gombe ta yi murabus
A wani labarin kuma Rikici Na Kara Tarwatsa PDP, Atiku Ya Yi Rashin Babbar Jigo a Jihar Gombe
Wata tsohuwar shugaba a jam'iyyar PDP reshen shiyyar arewa maso gabas, Mole Istifanus, ta fice daga jam'iyyar.
A wata wasika da ta aike wa shugaban PDP na gundumarta a jihar Gombe, ta gode wa kowa da kowa PDP bisa damar da aka bata ta bayar da gudummuwa.
Asali: Legit.ng