2023: Atiku Abubakar Ya Sake Magana Kan Rikicinsa da Wike, Yace Sun Matsa Gaba
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace ba zai yuwu a sauya shugabancin jam'iyyar PDP ba a yanzu
- Da yake tsokaci kan rikinsu da gwamnonin tsagin Wike, Atiku yace tuni ya daina damuwa kan batun ya matsa gaba
- Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP da Ayu na takun saka da Wike, wanda ya matsa lamba a canza shugaban jam'iyya
Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace tuni ya matsa daga kan batutuwan dake zama barazana ga damar jam'iyyar na lashe babban zaɓen 2023.
Jaridar Daily trust ta tattaro cewa aƙalla gwamnoni 5 ne suka matsa lamba suna kiran a sauya shugabancin babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa.
Gwamnonin waɗanda suka tsame kansu daga tawagar kamfen Atiku, sun ba da sharaɗin tuɓe Sanata Iyorchia Ayu daga kujarar shugaban PDP a matsayin hanya ɗaya tilo ta samun zaman lafiya a jam'iyyar.
Ɗaya daga cikinsu, gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya fito fili ya ayyana goyon bayansa ga ɗan takarar APC, Bola Tinubu, a zaben shugaban ƙasa mai zuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Haka zalika, Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, a lokuta da dama ya bayyana cewa PDP ba zata kai ko ina ba tare da fusatattun gwamnonin ba.
Ba zai yuwu a sauya shugabanci ba - Atiku
A wata hira VOA Hausa, tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace ba zai yuwu a halin da ake ciki yanzu a sauya shugabancin jam'iyyar PDP ba.
Atiku yace:
"Har yanzun bamu warware batun ba amma mun matsa gaba mun cigaba da harkoki, na daina damuwa da lamarin."
"A yanzu muna kan wata mahaɗa ce, ba zai yuwu mu tsaya magana kan sauya shugabanci ba yayin da zaɓe ke ƙara tunkaro wa da sauri."
Zamu magance matsalar tsaro - Atiku
Atiku ya ƙara da jaddada kudirinsa na dakile ƙalubalen tsaro da ya addabi kasa da zaran ya karɓi mulki a 2023.
"Zamu tunkari matsalar, zamu yi wa kwansutushin garambawul ta yadda jihohi da kananan hukumomi zamu basu karfin ikon tafiyar da harkokin tsaro."
"Kafin haka, zamu kara ɗaukar dakaru musamman yan sanda da jami'an Sibil Defens, duk zamu ingantasu da kayan aiki."
A wani labarin kuma Rikici Na Kara Tarwatsa PDP, Atiku Ya Yi Rashin Babbar Jigo a Jihar Gombe
Jam'iyyar PDP ta amince da naɗin Alhaji Salisu Lawal-Uli a matsayin shugaban reshenta na jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne yayin da sabon rikici ya ɓalle tsakanin ɗan takarar gwamna, Yakubu Lado da tsohon shugaba, Alhaji Majigiri.
Asali: Legit.ng