2023: Shugabannin PDP Sun Hargitse Bayan Wani Gwamna Ya Marawa Tinubu Baya

2023: Shugabannin PDP Sun Hargitse Bayan Wani Gwamna Ya Marawa Tinubu Baya

  • Abubuwan sun kara dagule wa a jam'iyyar PDP bayan kalaman gwamnan Oyo, Seyi Makinde, wanda ya nuna zai mara wa Tinubu baya
  • Wata majiya tace babu wani cikakken mamban PDP mai kishi da zai nuna murna kan yadda abubuwa ke tafiya
  • Sai dai mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, yace duk da haka jam'iyyarsu a dunƙule take

Oyo - Ga dukkan alamu shugabancin jam'iyyar PDP ya hargitse biyo bayan matakin gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo na ayyana goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu.

Daily Trust tace kafin wannan, Gwamna jihar Ribas, Nyesom Wike, ya goyi bayan kudirin neman tazarcen takwaransa na jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Makinde, Wike da wasu gwamnonin PDP uku da suka haɗa da, Okezie Ikpeazu na Abiya, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Samuel Ortom na Benuwai sun matsa lamba kan dole shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Jihar Arewa, Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a 2023

Bola Tinubu da gwamna Makinde.
2023: Shugabannin PDP Sun Hargitse Bayan Wani Gwamna Ya Marawa Tinubu Baya Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Da yake jawabi a wurin taron da ƙungiyar yarbawa Afenifere ta shirya domin Tinubu, mataimakin gwamnan Oyo, Bayo Lawan, wanda ya wakilci Makinde, yace mutanen Oyo zasu bi duk layin da shugabannin yarbawa suka bi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam'iyyar PDP ta shiga ruɗani bayan haka

Jaridar ta tattaro cewa waɗan nan abubuwan da ke faruwa sun dagula lissafin wasu shugabannin PDP. Wata majiya a Hedkwatar jam'iyyar tace, "Babu mai kishin PDP da ke murna da yanayin da ake ciki."

Haka zalika, wani mamban kwamitin gudanarwan PDP ta ƙasa (NWC),Tim Osadolor, yace gwamna Wike da masu goyon bayansa sun nuna cewa lallai su, "Marasa nasara ne."

Ya ƙalubalanci cewa ta ya wani mutum ɗan jam'iyya a cikin hankalinsa zai ayyana goyon baya ga ɗan takarar wata jam'iyya daban.

Yace:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta Kasa Ta Kori Ɗan Takarar Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Uku

"Idan kana fushi da Atiku Abubakar da Dakta Iyorchia Ayu, shin kana da matsala ne da jam'iyyar PDP reshen jihar Legas?"

Ya kuma zargi Wike da kulla-ƙullar yadda zai zama ɗan takara a zaɓen 2027 ta hanyar yaƙar Atiku da kuma yunkurin kwace ragamar jam'iyyar PDP bayan zaɓen 2023.

Har yanzun PDP a dunƙule take - Kakaki

Amma kakakin PDP, Debo Ologunagba, yace duk da kalaman da wasu gwamnonin jam'iyyar ke yi, har yau PDP a dunƙule take.

"Muna da matsala a cikin gida, muna ci gaba da kokari a kai, mai yuwa ka kalli abun na tafiyar hawainiya amma a wurin mu munsan sulhu na da tsawo mara iyaka, muna bin komai a hankali kuma tabbas kanmu a haɗe yake."
"Shin kunji wani ya nesanta kansa da zama mamban jam'iyya? Kowane lokaci suna faɗin su 'ya'yan jam'iyya ne, wasu daga ciki suna neman takara a inuwar jam'iyya. Mambobin mu ne kuma suna bayan jam'iyya."

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Samu Goyon Bayan Babbar Kungiyar Yarbawa da Gwamnan PDP

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Tona Asirin Abinda Yasa Shugaban PDP Bai Son Yin Murabus

Gwamna Wike yace hangen kuɗaɗen da PDP ka iya tarawa nan gaba ya hana Iyorchia Ayu yin murabus daga muƙaminsa.

Gwamnan jihar Ribas da wasu dake tare da shi sun ce ba gudu ba ja da baya har sai shugaban PDP ya sauka zasu mara wa Atiku baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262