2023: Tinubu Na Da Basirar Maida Shara Ta Zama Dukiya, Gwamna Lalong

2023: Tinubu Na Da Basirar Maida Shara Ta Zama Dukiya, Gwamna Lalong

  • Gwamna Simon Lalong na jihar Filato yace ɗan takarar APC, Bola Tinubu, na da kwarewar maida shara ta zama dukiya
  • Da yake jawabi a wurin wani taro a Legas, Lalong ya roki yan kasuwa da masu zaman kansu su mara wa takarar Tinubu baya
  • Sanata Ƙashim Shettima yace idan APC ta lashe zaɓen 2023, cikin wata Shida zuwa Shekara ɗaya zaman lafiya zai dawo

Lagos - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an bayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, a matsayin wani mutum mai basirar maida shara ta zama dukiya.

Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC kuma gwamnna jihar Filato, Simon Lalong ne ya faɗi haka wurin taron Tinubu da 'yan kasuwa wanda ke gudana a jihar Legas.

Gwamna Simon Lalong.
2023: Tinubu Na Da Basirar Maida Shara Ta Zama Dukiya, Gwamna Lalong Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Lalong yace Tinubu ya fi sauran masu neman zama shugaban ƙasa cancanta saboda yana da kyakkyawan tarihin canza abun da ya zama shara ya koma dukiya da kawo ci gaba.

Kara karanta wannan

"Zamu Kawo Karshen Matsalar Tsaro Cikin Watanni Shida" Tinubu Ya Faɗi Matakan Da Zai Ɗauka

"A wurin mu APC tallata Tinubu/Shettima ga yan kasuwa ba zai zama abu mai wahala ba saboda Asiwaju ɗan kasuwa ne da ya samu nasara wanda ya kawo ci gaba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya shirya tsaf domin kawo cigaba mai inganci ga 'yan Najeriya," inji gwamna Lalong.

Gwamnan ya roƙi yan kasuwan da masu zaman kansu su mara wa Bola Tinubu baya saboda ya ƙosa ya yi aiki tare da su da nufin samar da ayyukan yi da kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

Cikin wata shida zuwa shekara ɗaya zaman lafiya zai dawo - Shettima

A nasa jawabin, ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, yace da zaran sun ɗare mulki a 2023, gwamnatin Tinubu zata magance damuwar tsaro cikin watanni 6 ko shekara ɗaya.

A cewarsa, da zaran an rantsar da tsohon gwamnan Legas ɗin, zai haɗa tawagar da insha Allahu zata kawo ƙarshen ta'addanci baki ɗaya.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Tona Asirin Abinda Yasa Shugaban PDP Bai Son Yin Murabus

A wani labarin kuma Rikici Ya Sake Kunno Kai a APC, Hadimin Gwamnan Kwara Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Tsohon hadimin ya taka muhimmiyar rawa ba dare ba rana a tafiyar “O To Ge” da ta kai jam'iyyar APC ga nasara a zaɓen 2019.

Lamarin dai ya bude sabon shafi a siyasar jihar Kwara yayin da ake tsammanin Alhaji Musibau ka iya shiga PDP kowane lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262