2023: Shettima Yace Cikin Watanni Gwamnatin Tinubu Zata Dawo da Zaman Lafiya

2023: Shettima Yace Cikin Watanni Gwamnatin Tinubu Zata Dawo da Zaman Lafiya

  • Sanata Kashim Shettima yace idan suka lashe zaɓen 2023, gwamnatin Tinubu zata kawo karshen matsalar tsaro cikin wata 6
  • Da yake nasa jawabin, Bola Tinubu,ya faɗi wasu matakai da zai ɗauka da zaran ya shiga fadar shugaban kasa
  • A shekarar 2021, Tinubu ya nemi gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50,000 aikin soja da sauran hukumomin tsaro

Lagos - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar APC, Sanata Kashim Shettima, yace idan suka ci zaɓen 2023, gwamnatin Bola Tinubu, zata kawo karshen matsalar tsaro cikin watanni shida zuwa shekara ɗaya.

Shettima ya faɗi haka ne a wurin taron Bola Tinubu da 'yan kasuwa a jihar Legas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shettima tare da Tinubu.
2023: Shettima Yace Cikin Watanni Gwamnatin Tinubu Zata Dawo da Zaman Lafiya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

"A tsakanin watanni Shida da shekara ɗaya, shugaba na (Bola Tinubu) zai haɗa tawagar da zata kawo ƙarshen wannan rashin hankalin," inji shi.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Na Iya Maida Shara Mara Amfani Ta Zama Dukiya, Gwamnan Arewa

Haka zalika a nasa jawabin, ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matakan da zai ɗauka na magance matsalar da ta hana 'yan Najeriya zaman lafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane matakai zai ɗauka idan ya ɗare gadon mulki?

Tsohon gwamnan Legas ɗin yace gwamnatinsa zata kara yawan dakarun soji, da jami'an tsaro a dukkanin hukumomin tsaro da 'yan Sanda duk a wani ɓangare na tabbatar da zaman lafiya.

"Zamu ƙara ɗaukar mutane a hukumomin tsarom mu na Soji da 'yan sanda. Dakarun mu zasu samu nagartaccen horo kan dabarun sadarwa, iya tako, da ƙara inganta sintirin sama da ƙasa."
"Ta waɗannan matakan da ma wasu, zamu gano da kuma murkushe tawagar sheɗanun nan ko ina suka ɓuya. Ba zasu samu sa'ida ba har sai sun miƙa wuya ko an murkushe su."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming Pool

- Bola Tinubu

A 2021 yayin jawabinsa a wurin bikin karin shekararsa, Tinubu ya yi kira ga gwamnati ta zuba matasa miliyan 50 cikin hukumomin tsaro, lamarin daya haddasa cece-kuce.

Sai dai mai magana da yawunsa, Tunde Rahman, yace kalaman, "Subutar harshe ne," inda ya yi ƙarin haske da cewa mai gidansa na nufin matasa dubu 50,000.

A wani labarin kuma Gwamna Masari ya roki al'ummar jihar Katsina su yafe masa kura-kuran ya yi a zamanin mulkinsa

Gwamnan jihar Katsina ya roki ɗaukacin al'ummar Katsinan dikko da su yafe masa dukkanin kuskuren da ya aikata a mulkinsa.

Aminu Bello Masari, yayin kaddamar da kwamitin kamfen APC na jihar, yace akwai wasu mutane da suka nuna halin butulci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262