Daga Karshe Bola Tinubu Ya Amsa Bukatar Yan Najeriya, Ya fadi Hanyoyin Arzikinsa

Daga Karshe Bola Tinubu Ya Amsa Bukatar Yan Najeriya, Ya fadi Hanyoyin Arzikinsa

  • Bola Tinubu ya bayyana cewa yana daukar nauyin harkokin siyasarsa ne da kudin da ya samu bayan ya siyar da gidajen mansa guda biyu
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi bayanin cewa yana da gidajen mai guda biyu a Landan wanda matarsa ce ke kula da su
  • A cewar Tinubu, kudaden da ya samu daga siyar da kadarorin nasa sune ya yi amfani da su wajen daukar nauyin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO)

Abuja - Bayan yan Najeriya da dama a fadin duniya sun nemi jin ta bakinsa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya magantu kan tushen arzikinsa.

Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin kungiyar NAPOC a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa yana da gidajen gas biyu a birnin Landan, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

Tinubu
Daga Karshe Bola Tinubu Ya Amsa Bukatar Yan Najeriya, Ya faɗi Hanyoyin Arzikinsa Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Twitter

A cewar tsohon gwamnan na jihar Lagas, matarsa Remi ita ce ke kula da gidajen man wanda daga bisani ya siyar da su domin daukar nauyin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO).

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina da gidajen mai biyu a Landan, wanda matata ke kula da su. Na siyar da gidajen man biyu domin daukar nauyin harkokin rusasshiyar jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO)."

Bayanin Tinubu kan tushen arzikinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa watakila tsohon gwamnan ya yi wasu badakaloli kafin a sanshi a matsayin dan siyasa.

Da yake ci gaba da jawabi, Tinubu ya kuma bayyana cewa shi ya dauki nauyin NADECO tare da Alfred Rewane duk da cewar ya dade da mayar da hankali wajen zuba jari a kasuwanci daban-daban kafin ya shiga harkar siyasa.

Ana Wata Ga Wata: Ma'aikatan APC Sun Barke da Zanga-Zanga Kan Hakkinsu, Sun Nemi A Binciki Adamu

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Yi Ram da Gagararren Dilallin Kwayoyi

A wani labarin kuma, ma’aikatan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun koka kan cewa shugabancin jam’iyyar ya ki biyansu albashi.

Ma’aikatan jam’iyyar sun fusata ne bayan an amince da biyan alawus din gida da motoci ga mambobin kwamitin aiki duk da cewar ba a biyasu nasu albashin na watan Satumba ba har zuwa ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.

Yayin da babban sakataren APC na kasa, Felix Morka, ya yi ikirarin cewa an sasanta batun albashin ma’aikatan, ya bayyana cewa an samu tsaiko ne sakamakon wani tsari na cikin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng