Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Isa Akure Don Ganawa Da Shugabannin Afenifere
- Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya isa jihar Ondo don ganawa da shugabannin Yarbawa
- Tsohon gwamnan na jihar Lagas zai gabatar da manufofinsa ga Pa Reuben Fasoranti da shugabannin Afenifere
- Tinubu wanda ya samu tarba daga manyan jiga-jigan APC zai bayyana yadda zai kawo karshen matsalolin kasar da bunkasa tattalin arziki
Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Tinubu, ya isa Akure, babban birnin jihar Ondo.
Tinubu wanda ya isa jihar a yau Lahadi, 30 ga watan Oktoba, zai gabatar da manufofinsa ga Pa Reuben Fasoranti da shugabancin kungiyar Yarbawa ta Afenifere, jaridar The Nation ta rahoto.
Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya samu tarba daga gwamnan Ekiti, Abiodun Oyebanji, mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da sauran shugabannin APC, rahoton Punch.
2023: Al'amura Sun Canja Yayin Da Tsohon Ministan Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu, Ya Bada Dalili
Ana sanya ran Tinubu zai yi bayani kan yadda zam magance matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da ke fuskantar kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An tsaurara matakan tsaro a kewayen gidan Pa Fasoranti da ke Akure yayin da mambobin APC ke tururuwan zuwa yankin don yiwa Tinubu maraba da zuwa.
Dandazon jama’a sun marawa Tinubu baya daga filin saukar jiragen kaya na Akure zuwa gidan Farosanti, wajen taron shugabannin Afenifere.
Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023
A wani labarin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya magantu a kan yiwuwar hadakarsu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso gabannin zaben 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya bayyana cewa shi da kansa zai nemi Kwankwaso a daidai lokacin da ya kamata.
Tsohon gwamnan na jihar Borno wanda ke gabatar da jawabi a taron kungiyar limaman birnin tarayya Abuja, yana barkwanci ne da tsohon dan majalisar wakilai, Garba Ibrahim Muhammed, wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a taron.
Asali: Legit.ng