2023: Kar Ku Bari Mazajenku Su Zabi Wata Jam'iyya, Shugabar Matan APC
- Mataimakiyar Shugabar matan APC ta ƙasa, Zainab Lawal, ta nemi matan aure su tabbata mazajensu sun zaɓi APC a 2023
- A wurin kaddamar da wani Ofishin kamfe, Zainab ta ba mata shawarin su ɓoye katunan zaɓen mazan idan sun gano ba APC zasu zaɓa ba
- A cewarta, zaɓen wata jam'iyya da ba APC ba ɓata kuri'a ne da asara, suna bukatar samun nasarar raba ni da yaro a zaɓe mai zuwa
Abuja - Mataimakiyar shugabar matan jam'iyyar APC ta ƙasa, Zainab Lawal, ta yi kira ga ɗaukaacin matan Najeriya kar su bari mazajensu su zaɓi wata jam'iyya daban ba APC ba a babban zaɓen 2023.
Jaridar Daily Trust tace Zainab ta yi wannan kira ne a wurin kaddamar da Ofishin kamfe na ƙungiyar magoya baya "HUM National Support Group for Tinubu/Shettima" a Abuja jiya Asabar.
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya kaddamar da buɗe Ofishin a hukumance.
Zainab Lawal ta shawarci mata su kwace tare da ɓoye katunan zaɓen mazajensu idan sun san cewa zasu ɓata kuri'unsu ta hanyar zaɓen wata jam'iyyar daban da ba APC ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Lokaci ya yi da zamu hana jam'iyyar PDP bacci da dare, ku tabbata (duk wacce mijinta bai shirya zaɓen APC ba) kun ɓoye katunan zaɓensu, kar ku bari su yi asarar kuri'unsu."
"Wajibi baki ɗaya kuri'un da zasu kaɗa su tafi ga jam'iyyar APC, muna bukatar yin fintinkau ne mu samu nasara."
- Zainab Lawal.
A nasa jawabinsa, mataimakin shugaban APC na ƙasa daga arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya yaba wa shugaban ƙungiyar magoya bayan ta jam'iyyar APC.
Kyari ya gode mata bisa namijin kokarin da take wurin haɗa kan yan Najeriya su dangwala wa jam'iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
Ma'aikatan APC sun barke da zanga-zanga
A.wani labarin kuma Ma'aikatan APC Sun Barke da Zanga-Zanga Kan Hakkinsu, Sun Nemi A Binciki Adamu
An zargi shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) APC na kasa da yin babakere kan wasu kudade.
Ma’aikatan jam’iyyar wadanda suka koka kan rashin samun albashi tun watan Satumba sune suka yi wannan zargi kan shugaban nasu.
Asali: Legit.ng