2023: Ɗan Takara AAC Ya Kaddamar da Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Kano
- Ɗan takarar kujera lamba daya a Najeriya karƙashin jam'iyyar AAC ya kaddamar da kamfensa a birnin Kano
- Omoyele Sawore yace komai ya lalace a mulkin APC don haka lokaci ya yi da mutane zasu gano me yake musu ciwo
- Yace duk da halin kakanikayin da Najeriya ke ciki jam'iyyar AAC a shirye take ta kawo sauyi mai amfani
Kano - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar AAC, Omoyele Sawore, ya bude fagen yakin neman zabensa birnin Kano ranar Asabar
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa taron kaddamar da kamfen ya gudana ne a Kano Anti-Corruption Institute inda magoya bayan jam'iyyar suka tattaru.
Mista Sawore ya kuma bayyana manufofin jam'iyyar AAC tare da taimakon abokin takararsa Garba Magashi da ɗan takarar gwamnan Kano, Sani Yakasai.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ɗan takarar shugaban kasa na AAC, Onyinye-Gandhi Chukwunyere, ya fitar ranar Asabar, yace jam'iyyar ta tabbatar wa yan Najeriya, "Suna da 'yanci da kuri'unsu."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Chukwunyere yace:
"Daga nan babban birnin Kano mun kaddamar da kamfe ranar Asabar kuma zamu karaɗe lungu da sakon kasar nan don jan hankali da haɗa mutane kan aikin kawar da gurbatattun 'yan siyasa da dawo da ƙasa kan turba."
"Muna da yakinin cewa tare da goyon baya da haɗin kanku, AAC zata gina ƙasa ta yadda 'yan Najeriya zasu yi alfahari ta ita. Bisa haka AAC na mai tabbatar wa mutane duk wannan yanayin da suka shiga gyara na nan tafe."
Yan ta'adda sun mamaye mutane - AAC
Ya ƙara da cewa kusan yan ta'adda sun mamaye Najeriya ƙarƙashin gwamnatin jam'iyyar APC kana tattalin arziki ya shiga tsaka mai wuya, a cewarsa ba zata saɓu ba.
" A yau ƙasar mu ta fuskanci hanyar rugujewa, tattalin arziki na tangal-tangal tare da zaman kashe wando, ƙarancin Albashi, tashin farashin kayayyaki da sauran su."
"Yara sama da miliyan 20 suna gararamba a kan Tituna ba karatu, taɓarɓarewar tsaro ta ƙara kuntatawa mutane masu matsakaicin karfi, ta'addancin yan bindiga da sauransu, komai ya lalace a gwamnatin APC."
"Zamu sake nanatawa AAC ce kaɗai ta zo ta sake fasali ɗa kyawawan shirye-shiryen da zasu cika mafarkan mutane."
A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tinubu Kan Kalaman Zama a Dubai
Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 yace ba wanda zai yarda da Tinubu da APC.
Da yake martani kan kalaman Tinubu a Kano ta bakin kakakinsa Paul Ibe, yace mutane na tantama kan abubuwa da dama tattare da ɗan takarar na APC.
Asali: Legit.ng