Atiku Ya Dira Kasar Amurka Domin Zawarcin Manyan Jami'ai Kan Burinsa Na 2023

Atiku Ya Dira Kasar Amurka Domin Zawarcin Manyan Jami'ai Kan Burinsa Na 2023

  • Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, na ƙasar Amurka tun ranar Talata
  • Tsohon mataimakin shugaban zai gana da wasu Jami'an gwamnatin Biden domin neman goyon bayansu a 2023
  • Ana sa ran zai koma gida Najeriya bayan kammala zama da fitattun mutane wanda zai kai ranar Jumu'a

USA - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shilla ƙasar Amurka da yammacin ranar Talata a wani ɓangare na fafutukar cika burinsa a zaɓen 2023.

PM News ta ruwaito cewa, yayin zamansa a Amurka, Atiku da tawagarsa zasu maida hankali wajen zawarcin manyan jami'an ƙasar haɗi da fitattun mutane da nufin neman goyon bayansu.

Atiku Abubakar.
Atiku Ya Dira Kasar Amurka Domin Zawarcin Manyan Jami'ai Kan Burinsa Na 2023 Hoto: Atiku Abubakar/facebook
Asali: Facebook

Daga cikin tsare-tsaren Atiku yayin wannan ziyara a Amurka har da zama da manyan jami'an gwamnati wanda ya gudana ranar Laraba, a cewar rahoton Western Post.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnonin APC Biyu Sun Dira Patakwal, Sun Sa Labule da Gwamna Wike

Wasu 'yan ƙasar Amurka dake yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasan aiki ne suka nema masa zama da wasu manyan mambobin majalisar Amurka da jami'an gwamnatin shugaba Biden.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta gano cewa a shekarar 2019, Atiku ya yi makamanciyar irin wannan tafiya zuwa Amurka ana tsaka da yakin neman zaɓen kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Bugu da ƙari, wannan tafiya ta kasance ta farko da Atiku ya shiga Amurka tun bayan sauka daga mulki a 2017, kuma an shirya tafiyar ne domin ƙaryata jita-jitar ba ya iya shiga kasar saboda zarginsa da hannu a karkatar da wasu kuɗaɗe.

Dalilin tafiyar Atiku Amurka

Wata majiya tace Atiku ya yi wannan tafiya ne a wani ɓangare na kokarin ganin mafarkinsa na mulkin Najeriya ya zama gaskiya. Ana ganin cewa zama shugaban Najeriya na bukatar goyon bayan manyan kasahe irinsu Amurka.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tinubu Kan Kalaman Zama a Dubai

"Atiku ya amince cewa ba zai taɓa cika burinsa na mulkar Najeriya ba tare da samun goyon bayan ƙasashen waje ba musamman Amurka da Burtaniya."

"Wasu mutanensa sun samar masa da izinim gana wa da manyan jami'an gwamnati da mambobin majalisar ƙasar," inji majiyar.

An ce yayin ganawarsu, Atiku zai kokarin gamsar da su cewa idan ya kafa gwamnati zai kare kasuwanci da sauran muradansu a Najeriya da Afirka ta yamma.

Yaushe zai kammala ya dawo Najeriya?

"Atiku ya tsara dawowa gida bayan kammala tarukansa da jami'an Amurka wanda zai kai har zuwa ranar Jumu'a," cewar Majiyar.

A wani labarin kuma Rabiu Musa Kwankwaso Ya Magantu kan raɗe-raɗin zai janye wa wani takarar shugaban ƙasa a 2023

Kakakin kwamitin yakin neman zaɓe na jam'iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya musanta raɗe-raɗin Kwankwaso ka iya janyewa daga takara.

Johnson ya caccaki masu yaɗa jita-jitar inda ya bayyana cewa Kwankwaso zai gwabza a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Sarkin Ife Ya Angwance Da Amarya Ta 6 Cikin Wata Guda Kacal

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262