2023: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Murabus Daga Kujerarsa Bisa Sharadi Daya

2023: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Murabus Daga Kujerarsa Bisa Sharadi Daya

  • Gwamnan jihar Ribas Ya musanta cewa ya yi alƙawarin duk rintsi sai ya ɗora magajinsa yayin da wa'adinsa ya kare a 2023
  • Nyesom Wike ya sha alwashin murabus daga kujerar gwamna idan har aka kawo masa gamsasshiyar shaidar inda ya ɗauki alƙawarin
  • Babu cikakken bayanin da wa gwamnan yake amma dai ya yi wannan karin hasken ne domin kore ƙarerayin wasu mutane

Rivers - Gwamnan jjihar Ribas, Nyesom Wike, ya sha alwashin yin murabus daga kujerar gwamna matukar wani ya gabatar da gamsasshiyar shaidar dake nuna cewa ya ɗau alkawarin duk rintsi shi ne gwamna na gaba.

Gwamnan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kelvin Ebiri, ya fitar yau Talata 25 ga watan Oktoba, 2022.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
2023: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Murabus Daga Kujerarsa Bisa Sharadi Daya Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya jaddada cewa ba zai taɓa yuwuwa ya ɗaukar wa wani alƙawarin zama magajinsa kuma ya saɓa wannan alƙawarin ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan PDP Ya Caccaki Yan Takarar Shugaban Ƙasa Biyu, Yace Ba Zasu Kai Labari Ba a 2023

Jaridar The Nation tace Wike ya yi wannan jawabin ne a wurin taron da aka shirya domin murnar lambar yabon da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ba shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Allah ne kaɗai ke ba da mulki inji Wike

Gwamna Wike yace ya dace ya hito ya faɗi gaskiya game da zuƙi ta mallen da wasu mutane ke yaɗa wa, waɗanda suka yi ikirarin cewa ya musu alƙawarin zama magadansa.

"Allah ke ba da mulki, babu wata rana da na zauna da wani, ina kalubalantar kowaye yace mun zauna na ɗauki alkawarin cewa duba da yadda lamari ke tafiya kaine gwamnan mu na gaba."
"Idan har akwai wanda zai iya fitowa ya kalubalance ni to zan yi murabus daga matsayin gwamnan jihar Ribas."

- Nyesom Wike.

A wani labarin na daban Gwamnan Jihar Abiya Ya Sallami Wasu Daga Cikin Tawagar Hadimansa

Kara karanta wannan

2023: Babban Dalilin da Yasa Na Ɓoye Manufofina Ga Yan Najeriya, Kwankwaso Ya Magantu

Hadimai, mashawarta da wasu mataimakan kai da kai ga gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya sun rasa ayyukansu.

Rahoto ya nuna cewa an sanar da wasu hadiman gwamnan jihar Abiya su tsaya da aikinsu a daren ranar 24 ga watan Oktoba, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262