Gwamna Oyetola Ya Jagoranci Tattakin Kilomita Sama da 9 Don Nuna Goyon Baya Ga Tinubu
- Gwamnan jihar Osun ya fito ya jagoranci tafiyar kafa ta tsawon kilomita 9.2km a Osogbo domin nuna goyon bayan Tinubu
- Dandazon masoyan APC suka taru a gidan gwamnatin Osun da safiyar nan kafin fara tattakin bayan fitowar gwamna da tawagarsa
- Da yake jawabi bayan tattakin, Oyetola yace bai kamata yan Najeriya su mika Majeriya hannun waɗanda ba su san shugabanci ba
Osun - Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, mataimakinsa Benedict Alabi da wasu mambobin majalisar zartsawa sun jagoranci dubbannin masoya a Osogbo yayin tattakin nuna goyon baya ga Tinubu/Shettima.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa magoya bayan sun taru ne a gidan gwamnatin Osun dake Oke-Fia, Osogbo da misalin ƙarfe 9:00 na safe kafin daga bisani su tafi tattakin.
Gwamnan ya jagorancin tafiyar ƙafan ne daga gidan gwamnati aka ratsa ta titin Oke-Fia, Alekuwodo, Ola-Iya, Odi-Olowo, Isale-Osun, Oja-Oba, Titin Station, Ajegunle kana aka datse tattakin a Tashar Freedom.
Magoyan bayan na ɗauke da Banoni sannan sun sanya Hular hana Sallah mai ɗauke da Hoton ɗan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka zalika suna tafiya suna rera waƙa domin jawo hankalin mazauna jihar su kaɗa wa jam'iyyar APC kuri'unsu a babban zaɓen 2023 mai zuwa.
Bidiyon Tattakin Gwamna Oyetola
Gwamna Oyetola ya yi jawabi
Da yake jawabi a wurin da aka ɗiga aya a tattakin, Gwamna Oyetola ya ja hankalin magoya bayan su zaɓi Tinubu a zabe mai zuwa kuma su ci gaba da tallata APC.
Gwamnan yace:
"Tinubu zai zama shugaban kasar nan saboda bakuna masu tsarki sun ambaci haka. Ƙaurin sunan Tinubu ya kafu a jihar Osun, tun 1999 yake tare da mu, ya taka rawa wajen nasarar mu."
"Bai kamata yan Najeriya su bar ƙasar nan hannun wasu da basu san komai a shugabnci ba, dole mu zaɓi mutum mai kwarewa. Shi ne asalin wanda ya canza Legas."
A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tinubu Kan Kalaman Zama a Dubai
Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 yace ba wanda zai yarda da Tinubu da APC.
Da yake martani kan kalaman Tinubu a Kano ta bakin kakakinsa Paul Ibe, yace mutane na tantama kan abubuwa da dama tattare da ɗan takarar na APC.
Asali: Legit.ng