Shaidanun APC Sun Dade Da Komawa PDP, In ji Tsohon Minista
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa akwai banbanci tsakanin APCn da dana yanzu
- Fani-Kayode ya ce duk shaidanun da ke cikin jam'iyya mai mulki sun sauya sheka zuwa PDP
- Mamban na kwamitin yakin neman zaben shugabancin Bola Tinubu ya ce dole sai an dauki tsauraran matakai a kasar don cimma nasara
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa shaidanun da ke cikin jam’iyyar APC duk sun koma PDP tun bayan da ya dawo jam’iyyar mai mulki a watan Satumban 2021.
Fani-Kayode wanda ya kasance mamba a kwamitin yakin neman zaben shugabancin Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV.
Ya jadadda cewa sam APCn da dana yanzu ba daya bane akwai bambanci sosai.
Ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“APCn da ba ita bace APCn yanzu…Shaidanun da ke cikin APC a wancan lokacin sun sauya sheka sun kuma koma cikin PDP.
“Ra’ayina shine ra’ayina a wancan lokacin kuma abubuwa sun sauya lokacin da sabon shugabanci ya zo jam’iyyar, shugabanci nagari mai damuwa da ra’ayin mutane.”
Ya ce ya bar PDP ne saboda jam’iyyar ta zama azzalumar da yake zaton APC ce ita.
Ya kara da cewa a yanzu jam’iyyar mai mulki ta sauya “duk addininka, duk kabilarka.”
Tsohon ministan ya kuma ce ya zama dole Najeriya ta dauki tsauraran matakai idan har tana son ci gaba ta bangaren tattalin arziki, yana mai cewa akwai tallafi don rage radadin wadannan matakan.
Fani-Kayode ya ce dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu zai dakatar da abun da Buhari bai yi da kyau ba, rahoton Vanguard.
Kafin dawowarsa APC a shekarar bara, Fani-Kayode ya kasance babban mai sukar gwamnatin Buhari.
Bayan Sauya Sheka, Tsohon Sakataren Katsina Ya Bukaci Mutane Su San Yan Takarar da Zasu Zaba a 2023
A wani labarin, tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Dr. Mustapha Inuwa, ya gargadi gwamnatin jihar da manyan jami’anta da su daina takewa ma’aikata yancinsu na zaba ko hulda da yan takarar a suke muradi a zabe mai zuwa.
Inuwa ya kuma yi kira ga masu zabe da su kada kuri’unsu cikin hikima, Channels TV ta rahoto.
Tsohon SSG din ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Lahadi, a mahaifarsa ta Danmusa inda ya yanki tikitin kasancewarsa dan PDP, mako guda bayan ya sanar da ficewarsa daga APC tare da magoya bayansa.
Asali: Legit.ng