APC Ta Dakatar Da Tsohon Dan Majalisar Tarayya Da Tsohon Kwamishina
- Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Abia ta dakatar da tsohon dan majalisar tarayya, Uzo Azubuike
- Jam'iyyar ta kuma dakatar da tsohon kwamishinan kudi, Mista Obinna Oriaku duk kan zarginsu da cin amanar jam'iyyar
- A bangarensu, Oriaku ya bayyana cewa ba bai aikata wani laifi ba kuma wasu ne suka son koronsa daga jam'iyyar saboda ya kai kara kotu kan tikitin takarar gwamna
Abia - Shugabannin jam'iyyar APC a jihar Abia ta dakata da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar Aba ta Kudu da Arewa, Uzo Azubuike daga jam'iyyar.
Hakazalika, jam'iyyar ta dakatar da tsohon kwamishinan kudi, Mista Obinna Oriaku, rahoton The Nation.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dalilin dakatar da Azubuike da Oriaku
An dakatar da Azubuike, tsohon kwamishinan noma a jihar karkashin gwamnatin Gwamna Okezie Ikpeazu kafin ya koma APC da takwararsa na ma'aikatar Kudi, wanda shima ya koma APC daga PDP kan zargin cin amanar jam'iyya ne.
Sanarwar da jam'iyyar ta fitar kan korarsu ya ce an dauki matakin kansu ne saboda, "rahotannin rashin da'a da sakaci wurin ayyukansu duk da gargadi da jam'iyya ta musu, da kuma rashin nuna nadama duk da gargadinsu da aka yi su rika bin kundin tsarin jam'iyyar."
Shugabanin jam'iyyar sun kara da cewa an kore su ne bayan sahihin bincike da shawara daga kwamitin ladabtarwa da aka kafa a matakin mazaba da jiha, bisa tanadin sashi na Article 21B (i-v) na kundin tsarin jam'iyyar.
Ta kuma ce shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu, ba zai lamunci mambobi wadanda ke goyon bayan abokan hamayya ba da sauran ayyukan cin amanar jam'iyya.
Jam'iyyar ta gargadi saura masu irin wannan halayen su canja idan ba haka ba su fuskanci fushin kundin tsarin jam'iyyar.
Martanin Oriaku
Da ya ke magana kan dakatarwar, Oriaku a hirarsa da wakilin The Nation ya ce:
"APC na da tsari na hukunta mambobi da ke ayyukan anti party.
"A wasikar, ba a zargi Oriaku da wani laifin a zo a gani ba, kuma ba a gayyaci shi ko rubuta masa wasika kan batun ba.
"Laifinsa kawai shine ya tafi kotu kan ainihin dan takarar gwamna na jam'iyyar a jihar.
"Wasu na fargabar hukuncin da hedkwatar jam'iyyar na kasa za ta yanke a Abuja kuma suna son daukan mataki kafin lokacin.
"Su sani ba wani mutum daya da ke da APC. Wannan saba dokar ba zai tabbata ba idan an je kotu.
"Oriaku har yanzu dan APC ne. Shi yazo na biyu a zaben fidda gwani da Ikechi Emenike ya yi kuma ba za a kore shi daga jam'iyyar ba."
Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe
Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.
Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.
Asali: Legit.ng