2023: Matakai Kaɗan Suka Rage Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu
- Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Tinubu, yace sauran kaɗan ya gaji kujerar Buhari
- A wurin taro da Malaman Ɗarikar Tijjaniyya a Kano, Ɗan takarar na APC yace Addu'ar Malamai ce ke tare da shi
- Da yake tsokaci kan kalaman kabilanci da Atiku ya yi a Kaduna, Tinubu yace ɗan takarar ya tsame kansa daga tseren
Kano - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyya mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace saura matakai kaɗan ya zama shugaban kasa na gaba a Najeriya.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya yi wannan furucin ne a wurin tattaunawa da shugabannin Ɗarikar Tijjaniyya a jihar Kano.
Tsohon gwamnan jihar Legas yace tare da Addu'o'in Malamai da Allah ya riga ya amsa Wasu 'yan matakai ƙalilan suka rage ya zama shugaban ƙasa.
A kalamansa yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Da yawanku mun tattauna kuma kun sa mana albarka tare da Addu'a. Zaku yi Alfahari cewa ina tsaye a gabanku yayin da saura matakai kaɗan na ɗare shugaban kasa, Saboda haka Allah ya amsa addu'o'inku."
Atiku ya tsame kansa daga cikin tsere - Tinubu
Da yake martani kai tsaye ga kalaman Atiku Abubakar na tarwatsa haɗin kan ƙasa, Tinubu yace ɗan takarar na PDP ya tsame kansa daga tseren gaje kujerar Buhari.
"A tsakaninmu baki ɗaya, mu uku ne muka rage. Ɗaya ya faɗi ɓangare mai muhimmanci a jarabawa. Kai mai haɗa wa ne ko me tarwatsa wa? Yace ni ɗan arewa ne, kai mai tarwatsa haɗin kai ne."
Tsohon gwamnan ya ba da tabbacin cewa zai gyara tare da iza ƙasar nan kan turbar ci gaba da habaka a ɓangaren tattalin arziki da sauran muhimman ɓangarori, Punch ta rahoto.
A wani labarin kuma Gangamin Taron Kamfen PDP a Edo Ya Sake Fito da Rikicin Jam'iyyar, Atiku Ya Shiga Matsala
Gangamin taron yakin neman zaɓen shugaban kasa na PDP da ya gudana a jihar Edo ya kara fito da rikicin jam'iyyar.
Wasu gwamnoni dake kan madafun iko 5 sun kaurace wa taron, wasu kuma sun halarta ranar Asabar.
Asali: Legit.ng