Na Yi Kama Da Mara Lafiya? Takarar Shugaban Kasa Nake Nema Ba Gasar Yan Dambe Ba, In ji Tinubu
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya magantu kan rade-radin cewa bashi da cikakkiyar lafiya
- Tinubu ya yi watsi da rade-radin inda ya ce takarar shugabancin kasa shi yake nema ba wai gasar yan dambe ba
- Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ce abokan adawa ne ke yada batun don sun ga ya fi su hikima
Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi watsi da rade-radin cewa bashi da cikakkiyar lafiya.
Yayin da yake jawabi ga taron jama’a a ranar Asabar, 22 ga watan Oktoba a jihar Kano, Tinubu ya ce shi takarar shugabancin kasa yake nema ban a yan dambe ba.
Tsohon gwamnan na jihar Lagas cikin raha ya tambayi taron jama’ar da ke wajen kan ko ya yi kama da mara lafiya.
Tinubu ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba takarar tseren gudun sahu 100 ko 500 nake yi ba. Tseren neman shugabanci kasa nake yi. Ba takarar dambe na WWE nake yi ba.
Koda sun ce bashi da lafiya, gani tsaye a gabanku. Shin na yi kama da mutumin da bai da lafiya?”
Tinubu ya ce masu shirya wannan makirci sun tsorata da shi ne domin suna ganin shi din ya fi su hikima.
Kalli bidiyon a kasa:
Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano
A gefe guda, mun kawo cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da tallafin naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Kano.
Nigerian Tribune ta rahoto cewa Tinubu ya sanar da bayar da tallafin ne a wajen taron cin abincin dare wanda kungiyar yan kasuwa ta Kano ta shirya masa a ranar Asabar.
Tinubu ya ce ya bayar da tallafin ne domin rage radadi ga wadanda lamarin ya ritsa da su a kananan hukumomin jihar.
Asali: Legit.ng