KAI TSAYE: Dan Takarar APC, Bola Ahmad Tinubu Na Kaddamar da Manufofinsa na Kamfen
A yau ne Juma'a 21 ga Oktoba dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ke kaddamar da manunofinsa na kamfen gabanin babban zaben 2023.
A tun farko Tinubu ya yada a shafinsa na Twitter cewa, da misalin karfe uku na yammacin yau dinnan za a fara gudanar taron.
Ku kasance da Legit.ng Hausa domin kawo muku cikakken rahoton yadda taron ke gudana kai tsaye daga babban birnin tarayya Abuja.
Tinubu ya ce mulkinsa zai kasance na matasa ne da mata, zai mai da hankali a kansu idan aka zabe
Wasu daga cikin alkawuran da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu ya gabatar sun hada da damawa da mata da matasa a mulkinsa.
A cewarsa, mata da matasa ne kashin bayan tafiyar kowace al'umma wajen tafiyar tattalin arziki, gina kasa, nishadantarwa da wassanni.
Ya kuma bayyana cewa, babu abin da zai daidaita a Najeriya matukar ba a gyara fannin wutar lantarki ba. Saboda haka, Tinubu ya ayi alkawarin kawo sauyi a fannin wutar lantarki.
Zan yi takarar shugaban kasa ne saboda ni na san hanya, inji Tinubu
A bangare guda, Tinubu ya yi alfahari da cewa, shi ya san hanyar tsira da ci gaba ga Najeriya.
Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana cewa, ya nemi shawari daga mutane da dama, kuma tabbas APC ce hanya mafi sauki wajen ciyar da Najeriya gaba.
Ya kuma tunawa 'yan Najeriya yadda ya sauya jihar Legas ta zama tushen tattalin arziki sabanin yadda ya same ta a sadda ya hau kujerar gwamna.
Mutumin da ba zai iya gyara rikicin jam'iyya ba, ba zai iya rike Najeriya ba, Shettima ga Atiku
Abokin takarar Tinubu, kuma tsohon gwamnan Borno ya caccaki dan takarar jam'iyyar APC, inda ya bayyana cewa, Atiku bai cancaci zama shugaban Najeriya ba.
Da yake magana kan rikicin PDP dake kara ta'azzara, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Atiku bai da gogewa da zai iya daura Najeriya a kan turba duba da abin da ke faruwa a jam'iyyarsa.
Idan baku manta ba, ana ci gaba da kai ruwa rana da wasu jiga-jigan PDP tun bayan da Atiku ya zabe Okowa a matsayin abokin takara ba Wike ba.
An fara bayyana manufofin Tinubu, an fadi dukkan alheran da Buhari ya yiwa Najeriya
A daidai lokacin da jam'iyyar APC ta fara fadin bayyana abubuwan da zata cimma idan ta sake komawa mulki a 2023, ta fadi wasu daga cikin abubuwan da gwamnatinta ta cimma a karkashin jagorancin Buhari.