Jam’iyyar PDP Za Ta Gudanar da Taron Gangamin Kamfen Na Takarar Shugaban Kasa a Jihar Edo Ranar Asabar

Jam’iyyar PDP Za Ta Gudanar da Taron Gangamin Kamfen Na Takarar Shugaban Kasa a Jihar Edo Ranar Asabar

  • Jam'iyyar PDP za ta tattara ta shilla jihar Edo a ranar Asabar domin yin taron gangamin kamfen din tallata Atiku
  • Sanarwar da majiya ta samo ta bayyana cewa, ana kyautata zaton duk wasu jiga-jigan jam'iyyar za su halarci taron
  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da tallata 'yan takararsu na shugaban kasa gabanin babban zaben 2023 mai zuwa

Tawagar kamfen din tallata dan takarar shugaban kasan PDP za ta karkata zuwa jihar Edo a ranar Asabar 22 ga watan Oktoba domin gudanar da gangamin lasawa 'yan Najeriya alkawuran Atiku.

Rahoton da muka samo daga jaridar Punch ya bayyana cewa, ana sa ran duk wasu jiga-jigan PDP za su hallara a filin taro da misalin karfe 10 na safiyar ranar.

PDP za ta yi taron gangamin kamfen a jihar Edo ranar Asabar
Jam'iyyar PDP za ta gudanar da taron gangamin kamfen na takarar shugaban kasa a jihar Edo ranar Asabar | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Hakazalika, rahoton ya ce, dukkan gwamnonin da aka zaba a karkashin inuwar PDP za su hallara a wannan taro mai girma.

Kara karanta wannan

An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

Wannan batu dai na fitowa ne daga bakin babban daraktan gangamin kamfen din Atiku, gwamna Aminu Tambuwal, kamar yadda jaridar tace ta samo a jiya Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga-jigan da za su halarci taron

A cewar bayanin Tambuwal:

"Dukkan zababbun gwamnoni, mambobin kwamitin ayyuka na PDP, mambobin majalisar dokoki, mambobin majalisar zartaswa, 'yan takarar PDP da masu ruwa da tsaki za su kasance a jihar Edo domin gangamin kamfen na takarar shugaban kasa."

A cewarsa, za a yi taron ne a filin wasanni na Samuel Ogbemudia dake birnin Benin a jihar ta Edo.

Idan baku manta ba, ba a wanye da kyau a taron gangamin da PDP ta gudanar a makon nan ba a jihar Kaduna, lamarin da ya kai ga tashin-tashina da farmaki kan 'yan PDP.

Ya zuwa yanzu dai, dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar na can a birnin Landan, ba a san ko zai dawo kafin fara taron ba, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari

Allah Ya Yiwa Dan Sanata David Mark Rasuwa

A wani labarin, a yau muke samun labarin cewa, Allah ya yiwa babban dan Sanata David Mark, Tunde Mark rasuwa.

Wata majiyar dangi mai karfi ta bayyana cewa, Allah ya yiwa Tunde rasuwa ne a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba a asibitin birnin Landan ta Burtaniya.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, ana kyautata zaton cutar daji ce ta kashe Tunde, inji rahoton jaridar Daily Sun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.