2023: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar da Yakin Neman Zabe Kan Abu Daya
- Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP, Peter Obi, ya dakatar da kamfe ɗinsa na zaben 2023
- Tsohon gwamnan yace ba zai ci gaba da yakin neman zabe ba har sai ya ziyarci wasu yankuna da Ambaliyar ruwa ta afka wa
- Mista Obi ya bukaci sauran masu neman zama shugaba kasa su haɗa karfi da shi don jajatawa mutanen da lamarin ya shafa
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya dakatar da yakin neman zaɓen 2023, Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Obi ya sanar da wannan matakin ne yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja.
Ɗan takarar ya ɗauki wannan matakin ne a dai-dai lokacin da Ambaliyar ruwa ke ci gaba da jawo hasarar rayuka da dukiyoyi a jihohin ƙasar nan.
Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso
Ya kuma shawarci takwarorinsa masu neman kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar na PDP, Bola Tinubu, na APC da sauransu su haɗa kai wajen jajantawa mutanen da Ibtila'in ya taɓa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa yace:
"Kamar yadda kowa ya gani a yanzu, Ambaliyar ruwa na ci gaba da mamaye sassa daban-daban na kasar nan. Mutane na rasa rayukansu, wasu kuma na rasa matsugunansu."
"Ni a karan kaina na dakata kuma na gaya wa mutane na cewa ba sauran Kamfe har sai mun ziyarci wasu wuraren da lamarin ya shafa, aƙalla mu jajantawa mutanen da suka shiga jarabawa."
Meyasa Obi ya ziyarci gwamna Ortom?
Da yake jawabi kan dalilin zuwa wurin Ortom, Peter Obi yace:
"Na zo na nemi izini kuma na roke shi (Ortom) cewa ina son ziyartar wasu daga wuraren da Ambaliya ta yi ɓarna a jihar Benuwai kamar yadda nake shirin yi a wata jiha ɗaya ko biyu na daban."
A wani labarin kuma Gwamna Ortom yace da ace shi ba mamba bane a PDP da Peter Obi zai mara wa baya a zaɓen 2023
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana dan takarar da zai so goyawa baya a zaben shugaban kasa na 2023.
Ortom ya ce ba don shi dan PDP bane da zai yi kokarin ganin Peter Obi na jam’iyyar LP ya zama magajin Buhari.
Asali: Legit.ng