2023: Dalilin Da Zai Sa In Zabi Peter Obi Matsayin Shugaban Kasa, Sheikh Gumi

2023: Dalilin Da Zai Sa In Zabi Peter Obi Matsayin Shugaban Kasa, Sheikh Gumi

  • Shehin malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi mazaunin jihar Kaduna ya bayyana dalilan da zasu sa ya kadawa Peter Obi kuri’arsa
  • Gumi ya bayyana hirar da suka yi da Obi tare da tambayoyin da yayi masa kan tattalin arziki, ‘yan aware da sauran matsalolin kasar nan
  • ’Dan takarar jam’iyyar LP na kujerar shugabancin kasa, Peter Obi ya kai ziyara wurin babban malamin kafin fara taron da wasu kungiyoyin arewa suka nemi yi dasu

Kaduna - Fitaccen malamin musulunci dake zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, a ranar Litinin ya tarbi ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar Labour Party da mataimakinsa, Datti Baba-Ahmad a gidansa dake Kaduna.

Peter Obi da Gumi
2023: Dalilin Da Zai Sa In Zabi Peter Obi Matsayin Shugaban Kasa, Sheikh Gumi. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Obi ya halarci taron ganawa da ‘yan takarar shugaban kasa a Kaduna, wanda kwamitin hadin guiwan kungiyoyin Arewa ta shirya saboda gangamin zaben shekarar 2023, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Gana Wa da Manyan Arewa a Kaduna, Shugaban Jam'iyya Ya Mutu a Titin Kaduna-Zaria

Kwamitin hadin guiwan Arewan ya kunshi jiga-jigan wakilai daga kungiyoyin arewa kamar su Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Gidauniyar Ahmadu Bello (ABF), Kungiyar bincike da cigaban arewa da Jam’iyyar Matan Arewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron, wanda aka fara ranar Asabar, inda Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP, Kola Abiola na jam’iyyar PRP da Adewale na jam’iyyar SDP ne suka samu damar halarta a ranar.

Bola Tinubu, na jam’iyyar APC, Peter Obi na jam’iyyar Labour da na NNPP, Rabi’u Kwankwaso ne kwamitin ta bukaci ganawa dasu ranar Litinin.

Kwankwaso yayi watsi da batun halartar taron. A cewarsa, kungiyoyin da suka shirya taron sun zabi daya daga cikin ‘yan takarar.

Sai dai, kafin halartar taron, Obi ya kai wa Gumi ziyara tare da neman goyon bayansa gami da bayyana wa malamin abubuwan da ya shiryawa Najeriya idan aka zabesa shugaban kasa a zaben Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari

Malamin addinin musuluncin bai yi kasa a guiwa ba wajen da karo masa manyan tambayoyi game da farfado da tattalin arzikin kasar da yake gab da durkushewa da kuma magance matsalar bangaranci?

Inda Obi ya ce:

”Zan gyara tare da sake tsara Najeriya don su gane cewa babbar barazanarsu shine talauci.
“Kuma zan habaka babban tattalin arzikin kasa na arewa wanda shine noma.
“Talauci ne ya raba Najeriya kuma masu hannu da shuni na iya kokarinsu wajen ganin sun raba kawunanmu.”

Kwankwaso: Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba Kuma Ban Tura Mataimaki Na Ya Wakilci Ni Ba

A wani labari na daban, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa bai halarci bikin bude taron kungiyar lauyoyi na Najeriya, NBA, na 2022 da aka yi a Legas ba.

Rahotanni sun nuna cewa dan takarar APC, Bola Tinubu da Kwankwaso ba su halarci taron ba duk da cewa yan takarar shugaban kasa na manyan jami'iyyu a kasar sun hallarci taron da aka yi a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng