Jam'iyyar APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomin Jihar Osun Baki Daya
- Jam'iyyar APC ta lashe baki ɗaya kujerun Ciyamomi da Kansiloli da aka fafata a zaben kananan hukumomin jihar Osun
- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, Oladitan, shi ne ya ayyana yan takarar APC a matsayin zababbu
- Zababbun Ciyamomi da Kansilolin sun sha alwashin baiwa mara ɗa kunya dangane da amanar da al'umma suka ɗora musu
Osun - Rahoton da muka samu ya nuna cewa baki ɗaya 'yan takarar jam'iyyar APC da suka shiga zaɓen kananan hukumomin jihar Osun da aka kammala sun yi nasara ba tare da hamayya ba.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Osun (OSIEC), Segun Oladitan, shi ne ya bayyana haka a Osogbo ranar Lahadi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Mista Oladitan ya kuma miƙa takardar shaidar samun nasara ga 'yan takarar da suka lashe zaɓen kananan hukumomin duk a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba.
Shugaban OSIEC ya kara da cewa hukumar ta ayyana yan takarar a matsayin waɗanda suka samu nasara ne bayan cika kundin tsarin mulkin ƙasa da na dokokin zaɓe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane shirye-shirye hukumar ta yi kafin ranar zaben?
Oladitan yace tun a ranar Jumu'a 14 ga watan Oktoba, kwana ɗaya kafin ranar zabe, hukumar ta yi nazari tare da tabbatar da cewa babu wata takardar shari'a da ta haramta gudanar da zaben.
Da yake tsokaci kan rashin hitowar mutane, yace jam'iyyun siyasa ya kanata a ɗora wa laifi domin su ke da alhakin tallata yan takara da jawo hankalin masu kaɗa kuri'a ba hukumar zaɓe ba.
Wasu daga cikin zaɓabbun Ciyamomi da Kanasiloli sun sha alwaagin yin iya bakin kokarinsu domin futa daga kunyar mutanen da suka damka musu amana a yankunan su, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A wani labarin kuma Bayan Tawagar Wike, Wasu Gwamnonin PDP Hudu Sun Yi Barazanar Watsi da Atiku a 2023
Rikicin jam'iyyar PDP ya sake ɗaukar sabon babi yayin da wasu gwamnoni hudu suka haɗa kai don yakar Wike da makusantansa.
Gwamnonin sun yi barazanar janye wa daga kamfen Atiku idan har ya rasa mafita kuma ya sa Ayu ya yi murabus.
Asali: Legit.ng