Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotu Na Rushe Takarar Aisha Binani a 2023
- Jam'iyyar APC a jihar Adamawa zata ɗaukaka kara kan hukuncin Kotu na soke tikitin yar takarar gwamna a 2023
- A ranar Jumu'a, babbar Kotun tarayya dake zama a Yola ta rushe zaben fidda gwanin APC wanda Aishatu Binani ta samu nasara
- Sai dai APC tace ba zata yarda da matsayar Kotu na hana sake sabon zaben fidda gwani ba
Adamawa - Jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa tace zata ɗaukaka kara kan hukuncin da Kotu ta yanke wanda ya rushe zaben fidda gwanin da ya ayyana Aishatu Binani a matsayin yar takarar gwamna.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Babbar Kotun tarayya dake zama a Yola, babban birnin jihar Adamawa ta soke zaben fidda gwanin APC na takarar gwamna a 2023.
A hukuncin da Kotun ta yanke ranar Jumu'a, tace APC ta rasa damarta na tsayar da ɗan takara a zaben gwamnan Adamawa 2023.
Aishatu Binani, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya, ta yi nasarar lallasa Nuhu Ribadu, tsohon shugaban EFCC, da Jibrila Bindow, tsohon gwamnan jihar a zaben fidda gwanin da ya gudana a watan Mayu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane mataki APC ta shirya ɗauka kan lamarin?
Da yake tsokaci kan wannan ci gaban, Sakataren APC na jihar Adamawa, Raymond Chidama yace jam'iyya ta samu labarin cikin yanayi mara daɗi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Yace APC zata ɗaukaka kara kan hukuncin da Kotu ta yanke. Ya karada cewa:
"Bamu yarda da matsayar da Kotu ta ɗauka na hana gudanar da sabon zaben fidda gwani ba. APC zata bi duk wasu matakan neman adalci don tabbatar da nasara yayin ɗaukaka kara."
"Ina mai tabbatar wa mambobin mu cewa jam'iyyarmu zata gwabza a zaben gwamnan dake tafe a 2023 kuma ta samu nasara."
A wani labarin kuma An Samu Sabon Cigaba da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Jam'iyyar PDP Ta Ɗage Yakin Neman Zaɓe
Jam'iyyar PDP ta dakatar da yakin neman zaɓen shugaban ƙasa saboda danbarwar Atiku da gwamna Wike.
Atiku ya sake naɗa wata tawaga ta mutum uku masu faɗa aji a PDP da zasu shiga tsakaninsa da Wike don lalubo hanyar sulhu.
Asali: Legit.ng