Da Duminsa: Ayu Ya Magantu Kan Zargin Karbar Rashawar N100m da N1b
- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya amsa zargin da Gwamna Wike yake masa na karbar N100 miliyan daga Gwamnan PDP
- Ayu ya bayyana cewa Gwamnan ya bada kudin ne domin gyaran PDI wacce za a kaddamar cikin kwanakin nan kuma kudin ma basu kare ba
- A bangaren zargin karbar N1 biliyan daga ‘dan takarar shugaban kasa a Legas, Ayu yace bai karba ba amma da farko bashi aka ce za a ci na kudin
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya tabbatar da cewa ya karba N100 miliyan daga wani Gwamna.
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya zargi shugaban jam’iyyar na kasa da laifin rashawa inda yace baya da N100 miliyan da ya karba daga Gwamnan, Ayu ya karba N1 biliyan daga ‘dan takarar shugabancin kasa a Legas, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala taron yardaddu na jam’iyyar a hedkwatarta dake Abuja, Ayu yace batun N1 biliyan ya fara ne tun bayan da ya hau kujerarsa ina yana neman kudin rike kasa.
Yace jam’iyyar ta so karbar bashi amma an dakatar da hakan inda ya bayyana cewa bai karba wani kudi ba a matsayinsa na shugaban jam’iyyar na kasa.
A kan batun zargin N100 miliyan, Ayu yace kudin da ya karba daga Gwamnan PDP an yi amfani da su ne wurin gyara People’s Democratic Institute wacce za a kaddamar a cikin kwanakin nan.
Yace kudin basu kare ba kuma ya aike da wasika ga gwamnan da ya zo ya ga yadda aka yi amfani da kudin.
Rikicin PDP: Dalilin da Yasa Na Yi Murabus Daga Shugaban BoT Na Kasa, Jibrin Ya Fadi Gaskiya
A wani labari na daban, Nigerian Tribune ta rahoto cewa tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Walid Jibrin, ya magantu a kan murabus da yayi daga kujerarsa.
A farkon watan Satumba ne Jibrin wanda ya kasance tsohon sanata, ya sanar da murabus dinsa a taron BoT na PDP da ya gudana a Abuja.
Ya sauka daga kujerarsa ne a daidai lokacin da aka matsa lamba wajen kira ga sauya fasalin shugabancin jam’iyyar wanda ya baiwa yankin arewacin kasar fifiko.
Asali: Legit.ng