2023: Jam'iyyar ADC Ya Kori Tsohuwar Shugabar Majalisar Dokoki a Jihar Oyo
- Jam'iyyar ADC ta kori tsohuwar kakakin majalisar dokokim jihar Oyo, Monsurat Sunmonu, kan zargin cin amana
- A wata sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban ADC na jihar da Kakaki, jam'iyyar ta kori kwamishina mai ci da wasu jiga-jigai
- Sanarwan tace ADC ta yanke hukunci ne bayan mutanen sun goyi bayan tazarcen Seyi Makinde ba tare da neman izini ba
Oyo - Jam'iyyar African Democratic Congress, (ADC) ta kori mace ta farko da ta rike kujerar kakakin majalisar dokokin jihar Oyo, Monsurat Sunmonu, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
ADC ta ɗauki matakin korar Monsurat tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar saboda sun goyi bayan tazarcen Seyi Makinde, gwamnan jihar Osun na jam'iyyar PDP.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauki da sa hannun gamayyar shugaban ADC reshen Oyo, Adeoti Aderoju, da sakataren watsa labarai, Bimpe Adelowo.
Sauran Jiga-Jigan da ADC ta sallama daga inuwarta
Sauran waɗanda jam'iyyar ADC ta kora sun haɗa da kwamishinan yaɗa labarai, Michael Koleoso, da sauran mambobin jam'iyyar da gwamna Makinde ya ɗauka ya naɗa a gwamnatinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Niyi Adebisi, K.K. Obisesan, Kareem Toyin, Bunmi Olabode, Sola Oluokun, Oni Michael, Musibau Adejare, Fasto S.P. Akintokun, da kuma Bola Amusat duk suna cikin waɗanda ADC tattara musu komatsansu.
"Tun watan Disamba muke bibiyar abubuwan dake faruwa a cikin ADC, daga ciki har da (Korarrun mambobi) masu goyon bayan kudirin neman tazarce Seyi Makinde ba tare da neman shawari daga uwar jam'iyya ba," inji Sanarwan.
Siyasar Monsurat Sunmonu
Bayan rike kakakin majalisar dokoki, Monsurat, ta rike kujerar sanata mai wakiltar mazaɓar Oyo ta tsakiya daga 2015 zuwa 2019 karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Legit.ng Hausa ta gano cewa lokacin da take Sanata, Monsurat, ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar dattawa.
Ta tattara kayanta tare da wasu fusatattun mambobi sun fice daga APC zuwa ADC a shekarar 2018 bayan samun saɓani da Marigayi Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar.
A wani labarin kuma Sanatan PDP Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Faɗi Abinda Ya Faru Lokacin Marigayi Yar'Adua
Sanatan Adamawa ta kudu, Binos Dauda Yaroe, yace akwai bukatar sauya manyan shugabannin PDP na ƙasa.
Yaroe mai wakiltar mazaɓar da Atiku ya fito, ya roki tsagin Wike su yi koyi da abinda ya faru a 2007 lokacin marigayi Yar'adua.
Asali: Legit.ng