Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC

  • Jam'iyyar APC ta sanar da cewa tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya fice daga jam'iyyar
  • Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban kasa a APC yace tun makonnin da suka shuɗe jam'iyyar ta raba gari da Dogara
  • Dogara da Babachir Lawal na adawa da tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar APC

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki tace tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ba mambanta bane, ya jima da barin jam'iyyar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Yakubu Dogara.
Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Da yake martani kan rahoton cewa Dogara da wasu kusoshi sun zauna da Kiristoci da Musulman Arewa da nufin zaɓen ɗan takara daban da ba Tinubu ba su mara masa baya, Onanuga, yace Dogara ya bar APC makonnin da suka wuce.

Kara karanta wannan

2023: Kusoshin Kiristocin Jam’iyya Za Su yi Taron Dangi Domin Dankara Tinubu da Kasa

Yakubu Dogara da tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, sun jima suna kulle-kulle da ƙoƙarin jawo hankalin wasu 'yan Najeriya su ƙauracewa zaɓen APC a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manyan jiga-jigan siyasan biyu suna yin haka ne sabida jam'iyyar APC ta tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin dan takarar shugaban ƙasa da mataimaki.

Yaushe Yakubu Dogara ya fice daga APC?

Sai dai kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima yace:

"Yakubu Dogara, ɗan siyasa mara tabbas kuma wanda ya shirya taron ya fice daga jam'iyyarmu (APC) a hukumance tun wasu makonni da suka shuɗe kuma mahalarta taron don kansu ne da son ransu, ba Kiristocin arewa suka wakilta ba."
"Tun ƙafin haka, tsohon kakakin majalisar ke jagorantar fafutukar yaƙar jam'iyyarmu ta hanyar amfani da addini bayan gaza cimma burinsa na zama ɗan takarar mataimaki ga wanda ya fi shi cancanta, Sanata Kashim Shettima."

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

"Da muka yi nazari cikin natsuwa kan mutanen da suka halarci taron da ya kira mun gano cewa baki ɗayansu mambobin PDP ne, da ke bayyana kansu da 'ya'yan APC."

A wani labarin kuma Ƙarin Matsala Ga Tinubu, Jigon APC da Wasu Dubbannin Mambobi Sun Koma Bayan Atiku

'Ya'yan jam'iyyar APC mai mulki sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar adawa PDP a jihar Kogi.

Masu sauya shekan sun bayyana cewa jam'iyyar APC ta ba 'yan Najeriya kunya don haka lokaci ya yi mutane zasu farga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel