Da Duminsa: Bola Ahmed Tinubu Ya Diro Najeriya Bayan Kwashe Kwanaki a Turai
1 - tsawon mintuna
- Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, ya diro gida Najeriya a yau Alhamis, 6 ga watan Oktoba
- Tinubu ya bar gida Najeriya tun a ranar 24 ga watan Satumban 2022 yayin da ake haramar fara gangamin yakin zabe
- Jama’a sun ta cec-kuce tun bayan tafiyarsa ganin yadda bai halarci taron sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2023 ba
FCT, Abuja - Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC ya dawo Najeriya, Bashir Ahmad, hadimin Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Tinubu ya shilla ketare a ranar 24 ga watan Satumba kuma ya dawo Najeriya a ranar Alhamis.
Ganin karshe da aka yi wa ‘dan takarar shine a ranar 22 ga watan Satumba yayi da ya gana da manyan limaman cocin Pentecostal a Abuja.
A lokacin da baya kasar, jama’a sun damu da inda ya shiga ballantana da bai samu damar halartar taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2023 ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Karin bayani na nan tafe…
Asali: Legit.ng