Jiga-Jigai da Mambobin APC Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Kogi
- 'Ya'yan jam'iyyar APC mai mulki sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar adawa PDP a jihar Kogi
- Masu sauya shekan sun bayyana cewa jam'iyyar APC ta ba 'yan Najeriya kunya don haka lokaci ya yi mutane zasu farga
- Har zuwa yau dai jam'iyyar APC bata kaddamar da tawagar yaƙin neman zaben shugaban kasa ba saboda wasu dalilai
Kogi - Mambobin jam'iyyar APC sama da 5,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa Peoples Democratic Party(PDP) a jihar Kogi, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.
'Yan siyasan sun koma PDP ne ranar Lahadi a gundumar Avrugo da wata maƙotanta, ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu da ke jihar dake shiyyar arewa ta tsakiya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu, Honorabul Collins Adama, wanda ya jagoranci tawagar masu sauya shekar, yace APC ta ba 'yan Najeriya kunya.
A cewarsa, lokaci ya yi da 'yan Najeriya zasu kawar da gurbatattun shugabanni a zaɓen 2023, inda ya jaddada cewa idan mutane suka sake suka yi kuskure ko ya yake yanzun zai iya azabtar da ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adama, wanda ya samu tarba daga shugaban PDP na yankin Igalamela/Odolu, Hon. Attai Ndamusa Salifu, da ɗan takarar majalisar jiha, Umar Zakito, yace ya kamata APC ta tattara komatsanta daga jihar Kogi ta ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma yaba wa salon shugabancin masu ruwa da tsakin PDP a ƙaramar hukumar, haka kuma ya jinjina wa na matakin jiha da ƙaaa bisa zaƙulo 'yan takara masu nagarta da zasu iya share wa mutane hawayensu.
Ya kamata saura su yi koyi da ku - Hon. Attai
A nasa jawabin shugaban PDP na ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu, Hon Attai Salifu, ya ja jankalin sauran gundumomi da runfunan zaɓe su yi koyi da abinda ke faruwa a Avurgu.
Ya kuma kara da cewa jam'iyyar PDP ce zata zama zakara a babban zaɓen 2023 da ke tafe.
A wani labarin kuma Wani Gwamnan APC Ya Yi Magana Kan Bidiyon Tinubu Da Ake Yaɗa Wa a Kafafen Sada Zumunta
Gwamnan jihar Ebonyi yace ɗan takarar APC a 2023 ba ya bukatar dole sai ya tabbatar da yana raye.
Gwamna David Umahi yace rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah rashin lafiya kuma kowa da irin tasa.
Asali: Legit.ng