Da Dumi-dumi: Gwamnonin Jam’iyyar PDP 5 Sun Yi Ganawar Sirri A Enugu, Hotuna
- Gwamna Seyi Makinde na Oyo, Nyesome Wike na River, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwanyi na Enugu sun sa labule
- Ana ‘kishin-‘kishin cewa gwamnonin na PDP suna shirin marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi baya gabannin 2023
- Majiya tace sam hankalin gwamnonin bai kwanta da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar ba a zaben mai zuwa
Enugu - Wasu daga cikin manyan gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi wata ganawar sirri a jihar Enugu a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba, jaridar The Nation ta rahoto.
Jaridar Sun ta rahoto cewa tattaunawarsu ta karkata ne kan yadda zasu kawowa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Mista Peter Obi, kuri'u a zaben 2023.
Gwamnonin da suka halarci wannan zama sun hada da na jihar River, Nyesome Wike, Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benue.
Sauran sune gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu da takwaransa na jihar Enugu, Ifeanyi Ugwanyi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar wani na kusa da su, gwamnonin guda biyar na shirin marawa takarar Peter Obi baya ne saboda hankalinsu bai kwanrta da Atiku Abubakar ba.
Majiyar ta bayyana cewa wannan hukunci na gwamnonin baya rasa nasaba da rikicin da ya dabaibai babbar jam'iyyar adawar kasar ba.
Makinde da Wike na cikin mutanen da suka rura wutan cewa lallai sai shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga kan kujerarsa bisa hujjar cewa babu yadda za a yi yankin arewacin kasar ya rike manyan mukamai har biyu a lokaci guda.
Matashi Ya Zana Katafaren Hoton Peter Obi Jikin Bango A Jihar Kaduna, Yan Najeriya Sun Yi Martani
A wani labarin kuma, wani matashi dan Najeriya da ya shahara wajen yin zanen hotuna iri-iri, Bamaiyi Danladi, ya je shafin intanet don baje kolin wani hadadden aiki da yayi a Kaduna.
A wani bidiyo da ya yadu, matashin ya zana wani katafaren hoton dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a jikin wani bango a jihar.
Ya nuna yadda ya fara zanen har zuwa karshen hoton. Wannan baiwa tasa ta burge yan Najeriya da dama.
Asali: Legit.ng