Na Hannun Daman Gwamnan Arewa Da Daruruwan Magoya Baya Sun Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC
- Gabannin babban zaben 2023, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi babban kamu a jihar Sokoto
- Shugaban kungiyar magoya bayan Matawalle a jihar Sokoto da daruruwan magoya bayansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
- Jagoran masu sauya shekar, Alhaji Anas Waziri, ya bayyana cewa akwai karin 'ya'yan PDP da za su biyo su zuwa jam'iyyar mai mulki a kasar
Sokoto - Shugaban kungiyar magoya bayan Matawalle a jihar Sokoto, Alhaji Anas Waziri, da daruruwan masu mara masa baya sun sauya sheka daga People’s Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Bashar Abubakar, babban mai ba Sanata Aliyu Wamakko shawara a shafukan sada zumunta na zamani, a ranar Lahadi a Sokoto, PM News ta rahoto.
Abubakar ya nakalto Waziri yana cewa:
“Mun yanke shawarar barin jam’iyyar saboda shugabanninta sun gaza kaimu inda muke mafarkin zuwa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Barinmu PDP alamun nasara ne ga APC saboda karbuwar da ta samu a koina.”
Waziri ya bayyana cewa akwai karin mambobin PDP da za su biyo sahunsu zuwa APC.
Ya bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Alhaji Ahmad Aliyu a matsayin wanda yafi dacewa da mutanen jihar domin yana samun karin magoya baya.
Da ya tarbi masu sauya shekar, Aliyu ya fada masu cewa za a dama dasu kamar kowa a jam’iyyar.
Ya kuma dauki alkawarin tafiya da kowa a gwamnati idan har aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar, rahoton Daily Post.
Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Wasu 'Ya'Yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC Ana Tsaka da Rikici
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu mambobin jam’iyyar siyasa a jihar Oyo sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin babban zaben 2023.
Masu sauya shekar sun samu tarba a ranar Asabar yayin wani taron jam’iyyar da ya gudana a makarantar sakandare na Elekuro, Ogbere a yankin Ona-Ara da ke jihar.
Wadanda suka jagoranci taron na maraba da zuwa sune, Sanata Teslim Folarin, dan takarar gwamna na APC a jihar da Dr Yunus Akintunde, dan takarar sanata mai wakiltan Oyo ta tsakiya, PM News ta rahoto.
Asali: Legit.ng