Zaben 2023: Wasu Yan APC Suna Guna-Guni Kan Rashin Saka Sunan Tallen, Binani Da Wasu A Kungiyar Kamfen Na Mata

Zaben 2023: Wasu Yan APC Suna Guna-Guni Kan Rashin Saka Sunan Tallen, Binani Da Wasu A Kungiyar Kamfen Na Mata

  • Shirye-shiryen babban zaben shekarar 2023 na kara kayyatarwa da daukan hankula a yayin da zaben ke karatowa
  • Bisa alamu babban jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki za ta fuskanci matsaloli bayan fitar da sunayen kwamitin kamfen din kungiyar mata
  • An tattaro cewa ba a saka sunayen wasu jiga-jigai ba a jerin sunayen, hakan na iya haifar wa jam'iyyar matsala

FCT, Abuja - Wata kungiyar goyon baya ta jam'iyyar APC mai mulki a kasa, (APCSG), ta koka kan rashin saka sunan ministan harkokin mata, Pauline Tallen, Shugaban mata na kasa na APC, Dr Betta Edu, da yar takarar gwamna tilo a jam'iyyar, Sanata Aishatu Binani a kwamitin yakin zabe na mata na jam'iyyar.

Kungiyar, cikin sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba mai dauke da sa hannun Dingyadi Haruna ta ce hakan na nuna alamun jam'iyyar ta na dagewa ganin ta janyo rikicin cikin gida gabanin babban zaben na 2023, Legit.ng ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tonon Sililin Wike: Shugabannin PDP 4 Sun Mayar Kudi N122m Da Aka Basu

Tallen da Edu
Zaben 2023: Wasu Yan APC Suna Guna-Guni Kan Rashin Saka Sunan Tallen, Edu Da Wasu A Kungiyar Kamfen Na Mata. Photo: Pauline Tallen and Betta Edu.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunda farko, jam'iyyar ta APC a yau ta sanar da mambobin kwamitin yakin neman zaben na mata, inda First Lady, Aisha Buhari, Sanata Oluremi Tinubu, da Hajiya Nana, matar dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a matsayin jagororin tafiyar.

Jami'ar watsa labarai na kungiyar yakin neman zaben, Rinsola Abiola, yar marigayi MKO Abiola ce ta fitar da jerin sunayen yan kwamitin yakin neman zaben mai dauke da sunayen manyan mata da matan jiga-jigan yan APC guda 944.

"Rashin Sunan Tallen da Edu zai iya canjo rashin jituwa" - Haruna

Amma, Haruna wanda ya koka kan rashin sunan manyan mata masu muhimmanci a jam'iyyar daga kwamitin yakin neman zaben ya ce hakan na iya janyo rashin jituwa da rikicin cikin gida.

Ya ce:

"Wannan na faruwa a lokacin da jam'iyyar ke samun labarin soke takarar Gwamna Oyetola na Jihar Osun a matsayin dan takarar APC a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Yuli a jihar, bayan rawar da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Bala Buni, a matsayin shugaban kwamitin riko. Wani lauya na kundin tsarin mulki, Kayode Ajulo, ya ce hakan zai iya ruguza jam'iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Nan Babu Dadewa Wike da Tawagarsa Zasu Koma Wurin Tinubu, 'Dan APC Yayi Hasashe

"Idan za ka iya tunawa a baya-bayan nan gwamnonin APC, karkashin kungiyar gwamnoni da kwamitin ayyuka na kasa a baya, suma sun nuna rashin jin dadinsu game da sunayen yan kwamitin kamfen ba tare da sun samu wakilci ba."

Ya ce a yanzu ba a san dalilin da yasa APC ta dauki matakin watsi da jiga-jigan jam'iyyar masu magoya baya ba daga taka muhimmin rawa a kamfen din 2023.

Ya kara da cewa:

"Akwai yiwuwar APC za ta fuskanci babban matsala duba da cewa kamfen din 2023 ba zai samu daidaito ba irin na 2015 da 2019."

Kakakin Kamfen Ɗin Atiku Ya Fallasa Dalilin Da Yasa Osinbajo Da SGF Suka Ƙi Shiga Kwamitin Kamfen Ɗin Tinubu

A wani rahoton, Daniel Bwala, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya ce ya jinjinawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, SGF, saboda 'kin amincewa' da tikitin musulmi da musulmi na jam'iyyar APC.

Bwala ya yi wannan martanin ne kan rashin saka sunan Osinbajo da Mustapha daga jerin sunayen wadanda ke kwamitin kamfen din shugaban jam'iyyar APC na shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164