Malamin Coci Ya Yi Nadama, Ya Nemi Gafara Saboda Karbar Kudin Shan Ruwa a Hanya Daga Hannun Tinubu
- Bayanai dai na ci gaba da fitowa bayan da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya gana da malaman coci a Arewacin Najeriya
- An ce Tinubu ya ba malaman na coci 'kudin hawa mota' wanda hakan ya ba magoya bayansu da sauran 'yan Najeriya mamaki
- Wani malamin coci ya magantu, ya ce baya ga karbar kudin mota, sun tattaunawa kan batutuwa maso yawan gaske
Jihar Bauchi - Rabaran Danjuma Byang, mamba daga manyan malaman addinin kirista daga Arewa da suka wakilci tawagar Pentecostal wajen ganawa da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana kadan daga abubuwan da suka tattauna a kai.
Jairdar The Guardian ta ruwaito cewa, malamin ya rubuta wata wasikar nuna nadama a kafar WhatsApp, inda ya fasa kwai kan tattaunawarsu da Tinubu.
An zargi malaman na coci daga Arewa da cike aljifansu da kudi bayan da suka gana da Tinubu.
Amma Byang ya tabbatar da halartar malaman na coci, ya kuma yi bayanin cewa, shugabannin na addini sun ziyarci Tinubu don bayyana masa kokensu kan yadda ya dauko tafiyar siyasarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Na karbi na shan ruwa a hanya
Ya bayyana cewa:
"Tabbas, na halarci ganawar kuma na rubuta takaitaccen rahoto akai. Na yi mamakin yadda abin da suke iya karantawa kawai batun na karbi kudin hawa mota ne."
Malaman addinin kirista na ci gaba da sukar yadda Bola Ahmad Tinubu ya dauko tafiyar siyasarsa gabanin zaben 2023 mai zuwa nan kusa.
Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takara, lamarin da ya jawo cece-kuce daga kiristocin Kudu da Arewa.
Zan Jagoranci Najeriya Zuwa Ga Makoma Mai Kyau, Inji Dan Takarar APC Tinubu
A wani labarin na daban, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga abubuwan da ya shirya idan ya gaji Buhati bayan zaben 2023.
Ya matukar 'yan Najeriya suka zabe shi tare da abokin takarar sanata Kashim Shettima, to tabbas goben Najeriya za ta yi kyau ainun, Punch ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba 28 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa, zai shiga lungu da sakon Najeriya domin tallata hajarsa ga kwadayin dalewa kujerar Buhari.
Asali: Legit.ng