Gwamna Fayemi Na Jihar Ekiti Ya Rushe Majalisar Zaratarwan Gwamnatinsa

Gwamna Fayemi Na Jihar Ekiti Ya Rushe Majalisar Zaratarwan Gwamnatinsa

  • Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya sanar da rushe baki ɗaya majalisar zartarwan gwamnatinsa ranar Laraba
  • Wannan matakin na zuwa ne yayin da ake shirin rantsar da sabon zaɓaɓɓen gwamna mai jiran gado, Biodun Oyebanji
  • A ranar 16 ga watan Oktoba, 2022 gwamna Fayemi zai miƙa ragamar mulki hannun sabuwar gwamnati da mutane suka zaɓa

Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Dakta Kayode Fayemi, ya sanar da rushe baki ɗaya majalisar zartaswan gwamnatinsa yayin da ake shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a ranar 16 ga watan Oktoba, 2022 za'a rantsar da zaɓaɓɓen gwamna, Biodun Oyebanji, inda gwamnan zai miƙa ragama ga sabuwar gwamnati.

Taron majalisar zartaswan Ekiti.
Gwamna Fayemi Na Jihar Ekiti Ya Rushe Majalisar Zaratarwan Gwamnatinsa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Dakta Fayemi ya sanar da matakin rushe majalisar, wacce ta ƙunshi kwamishinoni da naɗe-naɗen gwamnati, yayin wani taro da ya gudana a Ofishin gwamnan a Ado-Ekiti.

Kara karanta wannan

2023: Jigon PDP a Kano Ya Tono Asalin Rikici, Yace Babu Hujjar Da Ta Nuna Atiku Ya Yi Wa Wike Alkawari

Ya umarci baki ɗaya masu rike da muƙamai su miƙa ragama ga babban ma'aikaci a ma'aikata, ɓangarori da hukumomin da suke.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Fayemi ya miƙa godiyarsa gare su baki ɗaya bisa goyon baya da gudummuwar da suka ba shi wajen dawo da martabar jihar Ekiti.

Mista Fayemi ya kuma yaba wa mambobin majalisar bisa sadaukarwar da suka yi ba tare da nuna son rai ba wajen kawo cigaba a jihar kana ya musu addu'ar Allah saka musu da mafificin Alheri.

Yace mutanen sun rubuta sunayensu baro-ɓaro da zinare kana ya musu fatan nasara a harkokin da zasu tasa nan gaba a rayuwarsu.

Mambobin majalisar sun gode wa Fayemi

Yayin taron, mambobin majalisar zartaswan jihar Ekiti sun ɗauki lokaci suna bayanin irin kwarewar da suka ƙara samu a tsawon shekaru hudu.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Jita-Jitar Wani Gwamnan PDP Ya Jingine Atiku, Ya Goyi Bayan Obi a 2023

Bayan haka kuma sun miƙa godiyarsu ga mai girma gwamna mai barin gado bisa damar da ya basu na yin aiki wa jiharsu.

A wani labarin kuma Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, ya yi bayanin dalilin da yasa Atiku ya fi dacewa ya karɓi Najeriya

Sambo, wanda ya halarci taron gabatar da litattafan Atiku da tawagar kamfe, yace ɗan takarar na da kwarewar da ake buƙata.

Sai dai ya shawarci jam'iyyar PDP ta haɗa kai sannan ta jawo kowa a jiki domin cimma nasara a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262