Lawal Ba Shi da Wata Kima, APC Ta Kasa a Yakinsa Lokacin Yana SGF, Oshiomhole

Lawal Ba Shi da Wata Kima, APC Ta Kasa a Yakinsa Lokacin Yana SGF, Oshiomhole

  • Kwamaret Adams Oshiomhole yace tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ba shi da tasiri ko a yankinsa
  • Da yake tsokaci kan banɗarewar Dogara da Lawal, Tsohon shugaban APC yace ba zasu rasa bacci ba kan waɗannan mutanen biyu
  • Lawal da Yakubu Dogara sun sha alwashin yaƙar APC a 2023 saboda tikitin musulmi da musulmi

Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Adams Oshiomhole, yace tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ba shi da wani tasiri a ƙaramar hukumarsa.

Oshiomhole yace jam'iyya mai mulki ta sha kaye a ƙaramar hukumar da take mahaifa a wurinsa lokacin yana kan kujerar Sakataren gwamnati, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwamaret Adams Oshiomhole.
Lawal Ba Shi da Wata Kima, APC Ta Kasa a Yakinsa Lokacin Yana SGF, Oshiomhole Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, Ya yi wannan furucin ne yayin hira da Channels tv cikin shirinsu na Politics Today.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan, Wike da Wasu Kusoshin PDP Ba Su Halarci Taron Kaddamar da Litattafai da Kamfen Atiku Ba

Lawal tare da tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, sun yi fatali da matakin ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Bola Tinubu, na ɗakko Kashim Shettima, wanda shi ɗin Musulmi ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga-jigan siyasar biyu tare da wasu jagororin Kiristoci, sun yi ikirarin cewa tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta ɗauka Wani yunkuri ne na dusashe tasirin mabiya Addinin kirista a arewa.

Da yake tsokaci kan jiga-jigan biyu, tsohon gwamnan yace jam'iyyar APC ta lashe zaɓe a 2019 duk da Dogara tare da Bukola Saraki sun sauya sheƙa zuwa PDP a lokacin.

A kalamansa yace:

"Abu ɗaya da na ɗaukar wa kaina alƙawari da matata kuma muka amince shi ne Adams, a wannan karon ba zai riƙa ambatar suna ba, ina son kawai na tada batun ne."
"A 2019, ana kakar babban zaɓen 2019, Dogara wanda ya ci zaɓe karkashin inuwar APC kuma ya zama kakakin majalisar wakilai a inuwar APC tare da Bukola Saraki suka ɗauki matakin koma wa PDP amma duk da haka muka ci zaɓe."

Kara karanta wannan

Muna magana da su PDP: Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari Yana Shirin Barin APC

Babachir Lawal bai da tasiri a yankinsa - Adams

"Babachir kuma, ku duba tarihi mun sha kaye a ƙaramar hukumarsa a 2015 da 2019 har lokacin da yake kan kujerar sakataren gwamnatin tarayya."
"Saboda haka idan har ba zai iya nasara a yankinsa ba duk da yana sakataren gwamnati to ba shi da tasiri. Shin kuna ga zamu ƙi huta wa ne saboda yanzu ya zama gwarzon kiristoci?"

- Adams Oshiomhole.

A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin Sunayen Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Da Suka Kaurace Wa Kaddamar da Tawagar Kanfen Atiku

Gwamnonin biyar ciki har da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, da wasu ƙusoshin PDP ba su halarci taron buɗe kamfen ɗin Atiku ba.

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da wani tsohon ministan duk ba'a gansu a wurin taron ba wanda ya gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262