Muna magana da su PDP: Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari Yana Shirin Barin APC
- Da alama kafar Injiniya Babachir David Lawal ta fara barin jam’iyyar APC saboda batun takara
- Tsohon Sakataren gwamnatin tarayyan Najeriyan yace magana tayi nisa da su da PDP, LP da NNPP
- Akwai yiwuwar tsohon shugaban majalisar wakilai na kasar nan, Yakubu Dogara ya bi Lawal
Abuja - Babachir David Lawal wanda ya taba rike sakataren gwamnatin tarayya da tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara suna daf da fita daga APC.
Wani rahoto da Punch ta fitar, ya nuna Injiniya Babachir David Lawal ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC a dalilin tikitin Musulmi da Musulmi.
Da aka yi hira da tsohon sakataren gwamnatin tarayyan, ya shaidawa manema labarai ba ayi wa kiristoci adalci a tafiyar APC ba, duk da irin yawansu.
A cewar Babachir David Lawal, har zuwa yanzu ba su dauki mataki a kan sauya-sheka daga APC, ko kuma su hakura suyi zamansu a jam’iyyar mai mulki ba.
APC ta ki mu - Lawal
Injiniya Lawan yake cewa su na tattaunawa da jam’iyyun hamayya irinsu PDP, LP da NNPP, yace APC ce kurum ta ki su a sanadiyyar tsaida Tinubu/Shettima.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An rahoto ‘dan siyasar yana mai cewa sun dauki wannan mataki ne saboda kishin Najeriya.
“A cikin jam’iyyun siyasa 18, muna magana da 'Yan Peoples Democratic Party, Labour Party da kuma New Nigeria Peoples Party.
APC ce kurum ta ki mu, amma sauran jam’iyyu 17 ba su ki mu ba. Saboda haka muna magana da ukun nan, ba a cin ma matsaya ba."
.... Cewar Babachir
Zaben 1993 dabam da zaben 2023
Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023
Kamar yadda Lawal yake fada, saboda MKO Abiola da Babagana Kingibe sun yi takara a 1993, bai nufin za a iya kara maimaita irin haka a zabe mai zuwa.
Lawal yake cewa duk da SDP ta zo gabar lashe zaben shugaban kasan 1993, amma an soke nasarar, yace mutane ba su nemi sanin asalin dalilin soke zaben ba.
Ina matsayar su Yakubu Dogara?
Da aka tuntubi Rt. Hon. Dogara ta wajen hadiminsa, Hassan Tukur, bai iya bada amsa a kan zaman mai gidansa a jam’iyyar APC ko zai shiga PDP, NNPP ko LP ba.
Rt. Hon. Dogara yana cikin 'ya 'yan APC da ke yakar tsaida Kashim Shettima da aka yi.
Shirin yakin neman zabe
Da farko an ji labari a ranar da aka soma kamfe, APC za ta shiga neman zabe gadan-gadan da yin addu’o’in samun nasara, yanzu an dakatar da wannan.
Wasu magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu da Abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima za su yi tattaki a tsakiyar Abuja domin ba ‘yan adawa tsoro.
Asali: Legit.ng