2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu
- Babban jigon PDP, Bukola Saraki ya magantu kan dalilinsa na kin cewa uffin a rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar
- Saraki ya bayyana cewa yana nan yana aiki a sirrince ta karkashin kasa domin kawo karshen rikicin Atiku da Wike
- Ya jaddada cewa Atiku Abubakar shine dan takarar shugaban kasa mafi alkhairi ga yan Najeriya a 2023
Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yi bayanin dalilinsa na yin shiru kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
PDP ta fada cikin rikici tsamo-tsamo tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawar kasar.
Rikicin ya kara kamari ne bayan Atiku ya yi watsi da Nyesom Wike, Gwamnan jihar Ribas a wajen zabar abokin takararsa.
Rikicin ya kara munana ne bayan makusantan Wike sun kauracewa aikin kamfen da aka daura masu, sannan suka ce lallai sai an cire Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar na kasa daga kujerarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duk da yawan taruka da aka gudanar don magance rashin jiyuwar, har yanzu abubuwa basu daidaita ba a jam’iyyar.
Yayin da yake jawabi a karon farko kan rikicin, Saraki ya ce yana ta aiki ta karkashin kasa, jaridar The Cable ta rahoto.
Ya ce:
“Yanzu nake dawowa daga hutun shekarana kuma kai tsaye Akwa Ibom na tafi don halartan taron cika shekaru 35 da kafa jihar.
“Yayin da nake zagayawa kasar a yan kwanakin da suka gabata, sai naga cewa mutane da dama sun damu da ganin cewa nayi shiru kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyarmu, PDP.
“Martanina shine cewa akwai lokacin da mutum zai yi magana kuma a ji shi sannan akwai lokacin da idan mutum na aiki ta karkashin kasa yafi yin tasiri. Yanzu ne wannan lokacin.”
Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kara da cewa Atiku shine yafi dacewa da yan Najeriya a 2023, rahoton Punch.
Shugaban Kasa A 2023: Peter Obi Na Kara Yin Suna Da Karfi, Babban Jigon APC Ya Yi Hasashe Mai Karfi
A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya magantu a kan karfin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ke samu gabannin babban zaben 2023.
Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook, yana mai bayyana bunkasar da Peter Obi ya samu a tseren shugabancin kasar a matsayin wani lamari da ke tattare da lauje a cikin nadi.
Ya tabbatar da cewar sunan Obi na tashi cikin sauri kuma yana kara samun karfi yayin da yayi hasashen cewa jam’iyyar LP za ta dare PDP a matsayin babbar jam’iyyar adawar kasar a zaben 2023 mai zuwa.
Asali: Legit.ng