Zaben 2023: Kwankwaso Ya Mamaye Mahaifar Shugaba Buhari, Ya Baiwa Mutane Mamaki
- Mai neman kujerar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara jihar Katsina
- Tsohon gwamnan jihar Kano ya buɗe sabuwar Sakatariyar jam'iyya mai kayan marmari a mahaifar shugaban ƙasa, Daura
- Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan, yace mutane sun fito kwansu da kwarkwata domin ganin ɗan takarar
Katsina - Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ziyarci jihar Katsina yau Lahadi, 25 ga watan Satumba, 2022.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya mamaye mahaifar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, inda ya buɗe sabuwar Sakatariyar NNPP a garin Daura, jihar Katsina.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka masa a ɓangaren kafafen sada zumunta, Saifullahi Hassan, ya fitar a shafinsa na Tuwita.
Sanarwan tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso (ranar 25 ga watan Satumba, 2022) ya buɗe sabuwar Sakatariya a mahaifar shugaba Buhari, Daura, jihar Katsina."
"Dandazon magoya bayan jam'iyyar ne suka yi tururuwa domin shaida buɗe sabuwar Sakatariyar."
Hotunan Kwankwaso a Daura
Legit.ng Hausa ta tattauna da wani Jigon NNPP, Mubarak Nalami Dabai, makusancin ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Bakori/Ɗanja, Eng Abdulrasheed Mansur Lambatu, wanda ya halarci tarukan jam'iyyar a Katsina.
Mubarak Dabai, wanda ya je Daura, Mashi, Mani, Malumfashi, Bakori da sauransu, ya faɗa wa wakilin mu cewa taro ya yi taro, Kwankwaso ya yaba da yadda Katsinawa suka nuna masa suna tare da shi.
Yace:
"Mun shiga Daura kuma mun ci masu garin da yaƙi, mu a Katsina NNPP muke yi kuma ita ke da nasara kowane mataki Insha Allahu."
"An wuce lokacin cewa jam'iyyu biyu gare mu a Najeriya, APC da PDP ba su da tashin hankali da fargabar da ta wuce NNPP duba da yadda ta taso da ƙarfi. Ko bamu kwace dukkan kujeru ba da izinin Allah zamu lashe kaso 75%."
A wani labarin kuma kun ji cewa Bola Tinubu da Uba Sani Sun Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Mambobin PDP a Kaduna
Gabannin zaben 2023, jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta rasa mambobinta masu yawan gaske a jihar Kaduna.
Dumbin mutanen da suka sauya sheka daga jam'iyyar adawar sun koma bayan Sanata Uba Sani da Bola Ahmed Tinubu na APC.
Asali: Legit.ng