Dalilin Da Yasa Na Yi Gum da Bakina Kan Rikicin Atiku da Wike, Bukola Saraki Ya Magantu

Dalilin Da Yasa Na Yi Gum da Bakina Kan Rikicin Atiku da Wike, Bukola Saraki Ya Magantu

  • Bukola Saraki yace yana iya bakin kokarinsa wajen kawo maslaha a jam'iyyar PDP ba tare da ya fallasa wa duniya ba
  • Tsohon shugaban majalisar Dattawan ya jaddada cewa har yau 'yan Najeriya ba su da zaɓin da zarce Atiku da PDP a 2023
  • Rikicin PDP mai adawa na ƙara tsananta biyo bayan kafewar tsagin Wike kan dole Ayu ya yi murabus

Tsohon shugaban majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya yi magana karon farko bayan tsawon lokaci, inda ya faɗi maƙasudin da ya sa ya yi gum da bakinsa game da rikicin jam'iyyar PDP.

A wani rubuta da ya saki a shafinsa na Facebook, Saraki, wanda bai jima da dawowa daga hutu ba, ya wuce kai tsaye zuwa jihar Akwai Ibom domin halartar bikin cikar jihar shekara 35 da kafuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan PDP, Gwamna Wike Ya Yi Sabuwar Tafiya

Bukola Saraki da Wike.
Dalilin Da Yasa Na Yi Gum da Bakina Kan Rikicin Atiku da Wike, Bukola Saraki Ya Magantu Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Tsohon Sanatan yace yana aiki tukuru ta bayan fage, inda ya ƙara da cewa akwai lokacin da ya dace ya fito ya yi magana kan batun.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda jam'iyyar PDP ke fama da rikicin cikin gida musamman kiraye-kirayen shugaban jam'iyya na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, na daga cikin ƙusoshin PDP da suka matsa lamba dole Ayu ya bar kujerarsa.

A baya-bayan nan, mutanen dake tsagin gwamna Wike suka sanar da janye jikinsu daga tawagar yaƙin neman zaɓe ta ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar.

Fusatattun mambobin PDP sun kafa hujjar rashin dai-daito da tura muƙamai yanki ɗaya a matsayin dalilinsu na matsa wa Ayu ya yi murabus, inda suka ce ɗan kudu ya dace ya zauna a kujerar.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023

Me Saraki ya faɗa kan batun?

Da yake martani a shafinsa na Facebook ranar Asabar, Saraki yace:

"Ban jima da dawowa daga hutu ba kuma na wuce kai tsaye zuwa jihar Akwa Ibom don halartar taron cikar jihar shekara 35 da kirkirowa. Yayin da nake zagaye sassan kasa na fahimci an shiga damuwa kan shirun da na yi a PDP."
"A fahimta ta akwai lokacin magana, akwai kuma lokacin da abinda ya fi dacewa ka yi shiru, ka yi ta aiki a bayan fage. Yanzu shi ne irin wannan lokacin."

Da yake tabbatar da goyon bayansa ɗari bisa ɗari ga Atiku Abubakar, Saraki yace, "A halin yanzu jam'iyyar PDP da Atiku ne mafi dacewa 'yan Najeriya su zaɓa a zaɓen 2023."

A wani labarin kuma Jigon Jam'iyyar PDP da Mambobi 200 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Delta

Jigon Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Delta ya jagoranci ɗaruruwan mambobi sun koma jam'iyyar APC ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Tura Mummunan Sako Ga Yan Najeriya Game da Zaɓen 2023, Wike

Prince Gabriel Nwanazia, yace ya ɗauki matakin koma wa APC ne saboda rikicin da PDP ke fama da shi wanda ya ƙi kare wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262