Ana Tsaka da Rikicin PDP, Gwamna Wike Ya Yai Sabuwar Tafiya Zuwa Turai

Ana Tsaka da Rikicin PDP, Gwamna Wike Ya Yai Sabuwar Tafiya Zuwa Turai

  • Gwamna Nyeson Wike na Jihar Ribas ya tafi wata ƙasa a nahiyar Turai awanni bayan fallasar da ya yi kan rikicin PDP
  • A ranar Jumu'a, Gwamna Wike ya yi hira da manema labarai inda ya taɓo batutuwan da suka shafi dambarwar PDP
  • Wannan na zuwa ne biyo bayan matakin 'yan tsagin gwamnan na janye wa daga kamfen PDP na takarar shugaban ƙasa

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya fice daga Najeriya zuwa nahiyar Turai bayan ya yi hira da manema labarai ranar Jumu'a, inda ya faɗi abinda ke ransa kan rikicin jam'iyyar PDP.

Yayin hirarar, gwamna Wike ya taɓo batutuwa masu yawa da suka haɗa da, tayin tikitin Sanata a 2023 da aka masa da kuma wani alkawari da Atiku Abubakar, ya ɗaukar masa a Landan.

Kara karanta wannan

2023: Karin Matsala Ga Atiku, Jigon PDP Da Ɗaruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Gwamna Wike na jihar Ribas.
Ana Tsaka da Rikicin PDP, Gwamna Wike Ya Yai Sabuwar Tafiya Zuwa Turai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan haka, Wike wanda ya jima yana neman shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus, ya faɗi dalilin da yasa yake son Ayu ya sauka da dai sauran batutuwa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wace ƙasa gwamnan ya nufa?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Gwamna Wike ya bar gida Najeriya zuwa wata ƙasa da ba'a ambata ba a nahiyar Turai da tsakiyar daren ranar Jumu'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta shaida wa wakilin jaridar cewa Wike ya bar filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas a wani jirgin sama da aka ware masa.

Bugu da ƙari, wata majiya daga gidan gwamnatin jihar Ribas, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya tabbatar da tafiyar gwamnan amma bai faɗi ainihin ƙasar da ya nufa ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Tura Mummunan Sako Ga Yan Najeriya Game da Zaɓen 2023, Wike

"Oga ya yi tafiya jiya da dare da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar dare amma ba zan iya cewa ga ƙasar da ya dosa ba," inji majiyar.

A wani labarin kuma Jigon Jam'iyyar PDP da Mambobi 200 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Delta

Jigon Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Delta ya jagoranci ɗaruruwan mambobi sun koma jam'iyyar APC ranar Asabar.

Prince Gabriel Nwanazia, yace ya ɗauki matakin koma wa APC ne saboda rikicin da PDP ke fama da shi wanda ya ƙi kare wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262