Rikicin PDP: Ina Nan Daram Tare da Gwamna Wike, Shugaban Yakin Zaɓen Atiku
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, yace ba abinda ya taɓa kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsa da Wike
- Gwamnan, wanda aka naɗa shugaban majalisar yaƙin zaɓen Atiku, yace kowa na da damar bayyana abinda ke ransa
- Emmanuel yace ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen sulhunta rikicin da ke faruwa a PDP kafin kaɗa gangar kamfe
Abuja - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, yace alaƙarsa da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na nan da kwarinta duk da wasu sun fara tsegumin jiga-jigan biyu sun yi hannun riga.
Gwamna Emmanuel ne aka naɗa shugaban tawagar yakin neman zaben shugaban ƙasa a PDP, amma Wike da ɗan takara, Atiku Abubakar ba su ga maciji.
Jaridar daily trust ta ruwaito cewa Atiku da Gwamna Wike sun fara nuna wa juna yatsa ne tun bayan ayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasan a matsayin wanda ya lashe tikitin PDP.
Da yake jawabi ranar Alhamis yayin amsa wasu tambayoyi a shirin Sunrise Daily na Channels TV, gwamna Emmanuel yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gwamna Wike ɗan uwana ne, kunsan da cewa alaƙar dake tsakanin mu na nan da kyau." Ya ƙara da cewa yana ci gaba da tattauna wa da gwamnan Ribas.
Wane matakai ake ɗauka na kawo karshen rikicin PDP?
Da yake martani kan janyewar tsagin Wike daga tawagar yaƙin neman zaɓe, gwamnan ya sha alwashin warware dukkanin matsalolin gabanin kaddamar da kamfe.
Yace gwamna Wike da yan tawagarsa na da damar bayyana mahangarsu, inda yace ba za'a yi watsi da buƙatunsu ba.
Babbar Bukatar Wike
Ɓangaren gwamna Wike sun bukaci shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi murabus, kana a maida kujerarsa hannun ɗan kudancin Najeriya.
An ce Ayu ya ɗauki alƙawarin sauka daga kujerarsa idan har ɗan arewa ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP amma a yanzun yana ikirarin shekara hudu aka zaɓe shi ya yi.
Amma gwamna Emmanuel yace ya zama dole 'yan Najeriya su koyi cika alƙawarin da suka ɗauka.
"Abu ɗaya da na fahimta a siyasa da rayuwa shi ne ya kamata mutane su yi kokarin aikata abinda bakinsu ya faɗa. Idan nace zan yi kaza idan A ta faru, ya dace na cika maganata."
"Idan nace za yi B matuƙar C ta faru, ya kamata na cika. Kowa na da yancin bayyana kansa yadda yake so. Daga lokacin da a matsayin ƙasaa muka koyi cika alƙawurra daga nan zamu ga dai-dai."
A wani labarin kuma Gwamnonin PDP Sun Bayyana Shirin Da Suka Don Magance Rikicin Atiku da Wike
Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal, yace nan ba da jimawa ba duk wannan rikicin zai zama tarihi a PDP.
Ya shaida wa mambobin BoT cewa shi da sauran takwarorinsa tuni suka fara laluben hanyar warware dukkanin saɓanin da suka yi wa jam'iyyar katutu.
Asali: Legit.ng