Ku Shawo Kan Matsalar Cikin Gida Kafin Ku Ceto ‘Yan Najeriya, Keyamo Ga PDP
Karamin Ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo, ya zundi jam’iyyar PDP kan rikicin da ke addabar jam’iyyar.
Keyamo ya ce jam’iyyar ta kasa shawo kan matsalolinta amma a kullum cewa take tana son ceto ‘yan Najeriya, The Punch ta rahoto.
Mai magana da yawun tawagar kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar APC ya duba wallafar da PDP tayi na daren Laraba
Wannan na zuwa me tsaka da lokacin da tsagin Gwamna Wike na jihar Ribas a ranar Laraba suka fice daga tawagar kamfen din PDP na kujerar shugaban kasa inda suka jaddada cewa Iyorchia Ayu yayi murabus kafin su shiga tawagar kamfen din.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Keyamo yayi mamakin yadda ‘dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da PDP ke ikirarin zasu ceto kasar yayin da suka kasa shawo kan matsalar cikin jam’iyyar da wuri.
A wallafar Keyamo:
“Jam’iyyar PDP dake cikin rikici saboda yadda ta kasa shawo kan matsalar da inuwar lema ke tattarowa kowacce rana da kuma abu na farko da suke fadin cewa zasu ceto Najeriya; kamar matashin da ya kafarsa ta kasa kaiwa kuloch din motar dake kokarin shiga gaban tirela! Wannan kamar sihri!”
Rikicin jam’iyyar PDP na cigaba da Kamari inda wasu ke kiran murabus don Ayu.
Buhari Ya Kawo Gagarumin Cigaba A Bangaren Samar Da Wutar Lantarki A Najeriya, In Ji Femi Adesina
A wani rahoton, Gwamnatin Tarayya a daren ranar Talata ta ce wutar lantarki ta inganta a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari matuka idan aka kwatanta da yadda ta ke a shekarun baya.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV.
Adesina ya ce kwantiragin da gwamnatin tarayya ta yi da kamfain Siemens ne yasa ake kawo transifoma da wasu kayan lantarki don magance matsalar dauke wuta a kasar.
Asali: Legit.ng