Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom Ta Ayyana Kujeru Biyu a Matsayin Babu Kowa

Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom Ta Ayyana Kujeru Biyu a Matsayin Babu Kowa

  • Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta ayyana kujerun wasu yan majalisu biyu da babu koma bayan sun sauya sheka
  • Shugaban majalisar, Aniekan Bassey, yace sun ɗauki matakin ne bisa hujjar tanadin doka a kundin mulkin Najeriya
  • Bayanai sun nuna cewa mambobin majalisar da matakin ya shafa sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa YPP

Akwa Ibom - Majalisar Dokokin jihar Akwa Ibom ta ayyana kujerun wasu mambobinta guda biyu a matsayin babu kowa a zaman ranar Talata.

Channels tv ta ruwaito cewa kujerun sune mazaɓar Esit Ekit da mazaɓar Ikono, kuma majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan masu wakiltar mazaɓun sun sauya sheka daga PDP zuwa YPP.

Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom.
Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom Ta Ayyana Kujeru Biyu a Matsayin Babu Kowa Hoto: channelstv
Asali: Depositphotos

Kafin ɗaukar wannan matakin, Usoro Akpanusoh, shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Esit Ekit yayin da Asuquo Nana Udo, ke wakiltar mazaɓar Ikono.

Kara karanta wannan

INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023

Yayin ayyana kujerun da babu kowa, kakakin majalisar, Aniekan Bassey, yace sun kafa hujja da sashi na 109 (1) (A-G) dake kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka yi wa garambawul.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace sashin dokar ya ƙunshi cewa, "Mutumin da ya kasance ya ɗare kujerar majalisar ta hanyar ɗaukar ɗawainiyar wata jam'iyya, daga baya ya koma wata jam'iyya ta daban gabanin zangon mulki ya ƙare."

"Sai dai idan ya koma sabuwar jam'iyyar ne sakamakon rabuwar kai a tsohuwar ko kuma jam'iyyun sun yi maja guri ɗaya da asalin jam'iyyar da ta ɗauki nauyinsa har ya ci zaɓe."

Bugu da ƙari, kakakin ya umarci Sakataren majalisa, Mandu Umoren, ya sanar da dukkan hukumomin da ya dace matakin da suka ɗauka, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Meyasa aka ayyana kujerun da babu kowa?

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman, shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Aniefiok Dennis, yace shugabansu ya dogara ne da tanadin dokar sashi na 109 (1) (g) wajen ayyana kujerun da ba kowa.

Kara karanta wannan

ASUU: Kar Ku Kai Matasa Bango, Ba Zamu Iya Shawo Kansu Ba Idan Suka Tunzura, Wani Sarki Ya Gargaɗi Buhari

Yace kakakin ya ɗauki matakin ne bisa wannan doka bayan mambobi masu wakiltar mazaɓun sun yi watsi da matsayin da jam'iyyar PDP ta ɗora su

A wani labarin kuma Bayan Karewar Wa'adi, Wani Sanata Ya Fallasa Matakin da Suke Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari

Yan sanda sun ce sun kama wani babban ɗan bindiga da ya addabi mutane, Umar Namaro, a jihar Zamfara.

Muhammed Shehu, kakakin yan sandan jihar yace dakaru sun kama wani Sojan Bogi ɗauke da muggan makamai a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262