NNPP 2023: Abba Gida Gida Ya Nesanta Kansa da Bidiyon Neman Kuɗin Kamfen
- Abba Gida Gida, mai neman kujerar gwamnan Kano a inuwar NNPP ya nesanta kansa da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta
- A wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Abba ya nemi ɗaukacin al'umma musamman mambobin NNPP su yi fatali da Bidiyon
- Faifan bidiyon da ake yaɗa wa ya nuna cewa ɗan takarar ya nemi masu niyya su haɗa masa N1,000 kowa don tara kudin kamfe
Kano - Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a 2023 karkashin inuwar NNPP mai kayan marmari, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya nesanta kansa da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta.
Bidiyon ya yi ikirarin cewa ɗan takarar ya nemi ɗaukacin al'umma da suka yi niyya su tallafa masa da N1,000 domin yaƙin neman zaɓe, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
ASUU: Kar Ku Kai Matasa Bango, Ba Zamu Iya Shawo Kansu Ba Idan Suka Tunzura, Wani Sarki Ya Gargaɗi Buhari
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ɗan takarar gwamnan ya roki ɗaukacin al'umma musamman mambobin NNPP su yi watsi da abinda Bidiyon ya ƙunsa.
Abba Gida Gida ya bayyana bidiyon da wata ƙarya da wasu marasa tarbiyya daga tsagin adawa suka ƙirƙira da nufin ɓata masa suna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwan tace:
"Mai girma ɗan takara (Abba Kabir Yusuf) na son sanar da al'umma cewa bai kirkiri wani tsarin tara kuɗi domin harkokin kanfe na zaɓen 2023 ba."
"Yada da kyau kowa ya sani cewa mai girma ɗan takara ya san da zaman abokanan Abba Gida Gida kama daga ƙungiyoyi a jami'o'in Najeriya, kwararrun masana doka da yan kasuwa waɗanda suka haɗa kansu da nufin samar da jagoranci mai kyau suke ganin ya dace."
"Muna nan kan bakarmu ba gudu ba ja da baya kuma mun sadaukar da kanmu domin ceto jihar Kano daga halin da kanawa suka tsinci kansu a ciki ƙarƙashin gwamnati mai ci ta mayaudara."
Kwankwaso ne shugaban kasan gobe - Jibrin
A wani labarin kuma Tsohon ɗan majalisar tarayya yace Atiku ba zai iya ja da Kwankwaso ba kuri'un mutanen arewa a zaɓen 2023
Abdulmumini Jibrin yace tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, na da damar lashe zaɓen shugaban kasa a 2023.
Tsohon ɗan majalisar yace Atiku na jam'iyyar PDP ba zai kama kafar Kwankwaso ba wajen samun kuri'u a arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng