Tsofaffin Hafsoshin Sojin Najeriya Uku Zasu Yi Wa Atiku Abubakar Kamfe a 2023

Tsofaffin Hafsoshin Sojin Najeriya Uku Zasu Yi Wa Atiku Abubakar Kamfe a 2023

Jam'iyyar PDP ta sanya sunayen tsofaffin shugabannin rundunar sojin Najeriya guda uku a cikin mambobin kwamitin yakin neman zaben ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Jam'iyyar PDP ta gayyaci tsofaffin Hafsoshin sojin Najeriya su yi wa ɗan takararta na shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, yaƙin neman zaɓe a 2023.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mutanen uku, Ishaya Bamaiyi, Kenneth Minimah da kuma Martin Luther Agwai, dukkansu Laftanar Janar ne masu ritaya kuma tsofaffin shugabannin hukumar Soji.

Kwamitin kamfe ɗin Atiku.
Tsofaffin Hafsoshin Sojin Najeriya Uku Zasu Yi Wa Atiku Abubakar Kamfe a 2023 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Haka zalika baki ɗayansu an gano sunayensu a cikin mambobin majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa (PCC) na PDP, waɗanda ke da alhakin tsara kamfe.

A ranar Alhamis, Sakataren tsare-tsare na PDP ta ƙasa, Bature Umar, ya sanar da mambobin tawagar kamfe din, wanda aka jima ana dako a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Matsala ga Atiku, Jigon PDP da Wasu Shugabanni Sun Yi Murabus, Sun Koma APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsofaffin Hafsoshin tsaron da suka shiga PCC

Ishaya Bamaiyi ya rike shugaban hukumar sojin ƙasa ta Najeriya daga 1996 zuwa 1999 karkashin shugabancin Marigayi shugaban ƙasa a mulkin soja, Sani Abacha, da Abdulsalami Abubakar.

Ɗan asalin garin Zuru a jihar Kebbi, Tsohon Sojan yana kan mulki lokacin da Najeriya ta canza daga tsarin mulkin soja zuwa mulkin demokaraɗiyya.

Duk da yana ɗaya daga cikin mambobin kwamitin amintattun PDP amma babu sahihin bayani kan lokacin da ya shiga jam'iyyar. Yana shiga harkokin PDP musamman a yankinsa arewa maso yamma.

Kenneth Minimah

Haifafen jihar Ribas, Kenneth Minimah, mutum na 268 daga cikin jerin mambobin majalisar kamfe ɗin Atiku, ya yi aiki a matsayin shugaban rundunar sojin ƙasa na tsawon shekara ɗaya.

Ya kasance a matsayin shugaban Soji daga shekarar 2014 zuwa 2015 lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan. Jaridar bata iya gano lokacin da ya shiga PDP ba bayan ya yi ritaya.

Kara karanta wannan

Ruwan Wuta: Jirgin Yakin Soji Ya Halaka Bashir Iblis da Wasu Ƙasurguman Yan Ta'adda a Arewa

A shekarar da ta gabata, Hukumar EFCC ta tuhumi Tsohon sojan, Minimah ɗan shekara 62 kan zargin karkatar da wasu kuɗi Biliyan N13bn da aka ware da nufin siyo makamai.

Martin Luther Agwai

A tsakanin 2003 zuwa 2006, Mista Agwai ya yi aiki a matsayin shugaban rundunar soji, dada baya ya zarce kujerar babban hafsan tsaro daga 2006 zuwa 2007.

A wani labarin kuma Gwamnan Arewa Ya Karɓi Ɗaruruwan Masu Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC Ciki Har da Ɗan Takarar Gwamna

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karɓi ɗaruruwan masu sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Daga cikinsu har da ɗan takarar da ya nemi tikitin gwamna a PDP, Abba Gana Tata, Buni ya nuna jin daɗinsa da sauya sheƙar jigon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262