Kotu Ta Umurci INEC Ta Amince Da Akpabio A Matsayin Ɗan Takarar Sanata Na APC

Kotu Ta Umurci INEC Ta Amince Da Akpabio A Matsayin Ɗan Takarar Sanata Na APC

  • Kotun tarayya a Abuja ta umurci hukumar zabe mai zamanta kanta na Najeriya, INEC, ta amince da Sanata Godswill Akpabio a matsayin dan takarar sanata na APC
  • Alkalin kotun, mai shari'a Emeka Nwite ya ce INEC ta saba doka a yayin da ta ki karbar sunan dan takarar da jam'iyyar ta APC ta mika mata
  • Tunda farko, tsohon ministan na harkokin Neja Delta ya yi murabus dafa aikinsa ne domin ya yi takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani na APC amma ya sha kaye

FCT Abuja - Wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta amince kuma ta wallafa sunan Godswill Akpabio a matsayin dan takarar sanata na jam'iyyar APC mai wakiltar Akwai Ibom ta Arewa/Yamma a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Duk Karya Ce, APC Tayi Watsi Da Zaben Yanar Gizo Na Cewa Peter Obi Yafi Samun Karbuwa

Mai shari'a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, ya ce INEC ta saɓa doka da ta ƙi karbar sunan Akpabio ta kuma wallafa duk da cewa jam'iyyar APC ta aika da sunan a matsayin dan takararta, The Nation ta rahoto.

Sanata Akpabio
Kotu Ta Umurci INEC Ta Amince Da Akpabio A Matsayin Ɗan Takarar Sanata Na APC. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Nwite, wanda ya ce hukumar ta INEC ta saba doka, ya ce hukumar bata da ikon soke takarar wanda ya shigar da kara na biyu (Akpabio).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Don haka, ina bada umurnin wanda aka yi kara (INEC) ta wallafa sunan wanda ya shigar da karar na biyu a matsayin ainihin dan takara."

A karar da aka shigar gaban Nwite, APC da Akpabio sune masu kara na 1 da 2 yayin da INEC ce wacce aka yi kararta, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Allah Ya Yiwa Dan Sanata Kabiru Gaya Rasuwa a FCT Abuja

INEC, a baya-bayan nan ta gargadi APC kan zabin dan takarar sanata na Akwa Ibom ta arewa/yamma.

Hukumar zaben ta ce sunan tsohon ministan na Neja Delta, Akpabio da jam'iyyar ta mika mata bai halasta ba sai ta bi ka'ida.

Udom Ekpoudom ya yi nasarar zama dan takarar jam'iyyar a zaben fidda gwani da aka ce jami'an INEC sun saka ido kan yadda aka yi a zaben.

Amma, jam'iyyar ta APC ta mika sunan Akpabio a madadinsa.

Kakakin INEC, Festus Okoye, a hirar da aka yi da shi, amma, ya ce hukumar ta ki amincewa da sunan tsohon ministan saboda ba shine aka zaba ba matsayin dan takara na yankin.

Bayan gaza samun tikitin Shugaban kasa, Jigon APC ya gagara samun tikitin Sanata

A wani rahoton, tsohon Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio ya gamu da tasgaro a yunkurin sa na zama ‘dan takaran Sanata a jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Babu Wani Kulumboto da Sihiri da APC Zata yi Amfani da Shi Don Cin Zabe, Ortom

Premium Times ta kawo rahoto Godswill Akpabio bai yi nasara wajen karbe takara daga hannun tsohon mataimakin shugaban ‘yan sanda, Udom Ekpoudom.

Masu neman takaran Sanatan su na shari’a ne a babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164