Sokoto: Yadda Jam'iyyar PDP Tayi Babban Kamu, Dubban Mabiya APC sun Sauya Sheka
- 'Yan kasuwan kayan daki a kalla 1,868 dake jihar Sokoto ne suka sauya shekar daga jam'iyyar APC zuwa PDP
- Sun bayyana shugabanci nagari wanda Gwamna Tambuwal ke yi a jihar matsayin dalilin farko da yasa suka yanke wannan hukuncin
- 'Yan kasuwan sun ce jam'iyyar APC ta ci amanar 'yan Najeriya don haka zasu tabbatar da nasarar PDP a zabukan dake gabatowa
Sokoto - A kalla 'yan kasuwa 1,868 daga yankunan kasuwanci 10 na jihar Sokoto a ranar Laraba suka bar jam'iyyar APC tare da komawa jam'iyyar PDP.
Wadanda suka sauya shekar sun alakanta yin hakan da tsarin shugabanci nagari na Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal a matsayin daya daga cikin dalilan da yasa suka koma PDP.
A yayin jawabi a madadin masu sauya shekar, shugaban kungiyar 'yan kasuwar, Alhaji Lawali Aminu Lalala, yace sun sakankance kan irin shugabanci nagari da gwamnatin PDP a jihar Sokoto take yi kuma suna farin cikin hada guiwa da gwamnatin jihar wurin ciyar da jihar gaba.
Ya yi bayanin cewa, gwamnatin APC da suka zaba sun ci amanar 'yan Najeriya a kusan dukkan bangarori.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa, sun sha alawashin yin biyayya tare da goyon bayan PDP kuma sun yi alkawarin zaben 'dan takarar PDP a zabuka maus gabatowa.
A takardar da sakataren yada labarai na jam'iyyar a jihar ya saka hannu, Hassan Sahabi Sayinawal, yace yayin karbar masu sauya shekar, shugaban PDP na jihar Sokoto, Honarabul Bello Aliyu Goronyo wanda ya samu wakilcin shugaban PDP na shiyyar Sokoto ta tsakiya, Alhaji Muhammadu Dangoggo, ya tabbatar musu da cewa yanzu su cikakkun 'ya'yan jam'iyyar ne kuma daidai suke da tsoffin.
Takardar ta kara da bayyana cewa, shugaban ya yi alkawarin tafiya tare da kowa kuma yayi kira garesu da su yi amfani da gogewarsu a siyasa da kasuwanci wurin tabbatar da nasarar PDP a zabe mai zuwa.
'Yan Majalisa ga Gwamnoni: Motocin da Harsasai Basu Hudawa ba Zasu Kare ku daga Fushin Yaran Talakawa ba
A wani labari na daban, kwamitin wucin-gadi na majalisar wakilai kan ilimi a ranar Talata ya ja kunne gwamnonin kasar nan da su fifita ilimi ko kuma su shirya fuskantar kalubale.
Shugaban kwamitin , Farfesa Julius Ihonvbere, ya sanar da hakan a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a karshen ziyasar kwana biyu da ya kai na duba ayyukan hukumar UBEC da SUBEB ke yi a jihar.
"Ina son in shawarci gwamnatocin jihohi da su dauka ilimi da muhimmanci. Motocin da harsasai basu hudawa, karnuka da wayoyin zagaye gidaje ba zasu iya tseratar da su daga fushin yaran da ba a ilimantar ba, wadanda aka ci zarafi da kuma wadanda aka yi watsi da su."
Asali: Legit.ng