2023: Dalilin Da Yasa Ba Zamu Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Ba, Atiku
- Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, ta bakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa yace akwai gagarumar matsala idan aka sauke Ayu
- Kakakin Kamfen ɗin Atiku, Charles Aniagwu, yace PDP ta hango rikicin da ya zarce na yanzu idan ta aiwatar da bukatar Wike
- A cewarsa, dama abinda APC ke jira ta ga ya faru kenan amma masu ruwa da tsaki suka gano, yanzu ana ɗaukar wasu matakai
Abuja - Tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, ta bayyana cewa tunɓuke shugaban jam'iyya na ƙasa, Iyorchia Ayu, zai ƙara dagula rikici ne.
The Cable tace a ranar Alhamis, majalisar zartarwa ta PDP (NEC) ta kaɗa kuri'ar amincewa da Ayu duk da kirayen-kirayen da ake na ya sauka daga muƙaminsa kamar yadda ya alƙawarta.
Da yake hira da kafar Talabijin ta Arise TV, kakakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Atiku ta ƙasa, Charles Aniagwu, yace maimakon sauke Ayu, jam'iyya ta zaɓi bin wasu hanyoyin magance rikicin da ya addabeta.
"Zuwa yanzun jam'iyya ta lalubo hanyar warware matsalolinta, amma bari na kara bayani kan batun sauke shugaban PDP na ƙasa, an wuce wannan lamarin saboda NEC ta kaɗa kuri'ar kwarin guiwa kansa," inji shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ɗaiɗaikun mutane zasu iya gurguwar fahinta kan abinda aka yi, shugabannin PDP sun zauna sun duba tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam'iyya da aka yi wa garambawul a 2017."
"Idan ka duba wannan kundi, manyan shugabanni da ake kira kwamitin gudanarwa ƙarkashin jagorancin shugaban jam'iyya na ƙasa, bayan Ciyamun, mutum na gaba shi ne mataimaki kuma daga shiyyar da Ciyaman ya fito."
"Bayan waɗan nan sai kuma Sakatare na uku. Idan ka duba waɗannan muƙaman, shugaba na ƙasa ɗan arewa ne, mataimaki mai daraja ta biyu yankinsu ɗaya. Idan ka matsa sashi na 45 yace idan shugaba ya yi murbus mataimakinsa zai karɓi jagoranci."
- Charles Aniagwu.
Dalilin tsallake bukatar Wike - PDP
Kakakin Kamfen Atiku ya ƙara da cewa PDP ta duba batutuwa da dama kuma idan aka yi waɗannan canje-canje, jam'iyya ka iya afka wa cikin rikici mafi muni fiye da yanzu.
"Zaɓen shugaban ƙasa ya kusa, bamu son wayar gari ciki rikicin da sai dai a mana jaje kuma idan muka yi waɗan nan sauye-sauyen da yuwuwar mu shiga tarkon rikicin da yafi na yanzu muni."
"Wannan jam'iyyar APC ta zuba ido ta ga ya faru amma shugabannin mu suna da basira da hangen nesa kuma na ji daɗin yadda Wike da wasu jagorori suka yaba da kokarin jam'iyya."
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Fara Zawarcin Jiga-Jigan APC, Ta Dira Gidan Tsohon Sakataren Gwamnati
Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta fara zawarcin tsohon Sakataren gwamnatin Jiha, Dakta Mustapha Inuwa.
Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Sanata Lado Ɗanmarke, ya ziyarci Inuwa tare da rokon ya yafe abinda PDP ta masa a baya.
Asali: Legit.ng